✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mayakan ISWAP sun sace manoma 6 a Borno

Kungiyar ISWAP ta yi awon gaba da akalla manoma shida a kauyukan da ke kusa da garin Mafa da ke Jihar Borno a ranar Laraba.…

Kungiyar ISWAP ta yi awon gaba da akalla manoma shida a kauyukan da ke kusa da garin Mafa da ke Jihar Borno a ranar Laraba.

Wani jami’in leken asiri, ya shaida wa Zagazola Makama, kwararre kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a Tafkin Chadi, cewa akasarin wadanda harin ya rutsa da su ’yan gudun hijira ne.

Ya bayyana cewa mutanen sun bace ne bayan sun je gonarsu a kauyen Bulagarji, da ke kusa garin na Mafa.

’Yan uwan ​​wadanda lamarin ya rutsa da su, sun ce ’yan ta’addan sun far wa manoman ne da sanyin safiyar Laraba inda suka kai su wani wuri da ba a sani ba.

Daya daga cikin ’yan uwan ​​da ya nemi a sakaya sunansa ya ce ISWAP na neman kudin fansa Naira miliyan biyar kafin su sako wadanda abin ya shafa.

A wata mai kama da haka wasu masu garkuwa da mutane sun kashe wani Malam Muhammad, mazaunin bayan Jami’ar Maiduguri ranar Asabar 13 ga watan Agusta 2022.

Wani dan uwansa da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce masu garkuwa da mutanen sun kira iyalansa suka  bukaci a ba su kudi Naira miliyan biyar amma iyalansa suka ce ba za su iya tara kudin ba saboda Naira miliyan uku ne kawai za su iya tarawa.

Masu garkuwa da mutanen sun ki amincewa da kudin sannan daga bisani suka  kira iyalansa domin dauko gawarsa.

An yi jana’izarsa a ranar Laraba 17 ga Agusta 2022 kamar yadda addinin Musulunci ya tanada