✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Taliban sun watsa taron mata masu zanga-zanga

Mayakan Taliban sun lakada wa taron mata masu zanga-zangar neman ’yanci duka a birnin Kabul.

Mayakan Taliban sun lakada wa wasu mata duka saboda sun fito zanga-zangar neman ’yanci a Kabul, babban birnin kasar Afghanistan.

Mayakan sun fara yin harbi ne a iska domin tarwatsa taron matan a safiyar Asabar, gabanin cika shekara guda da dawowar kungiyar kan mulkin kasar, ranar 15 ga watan Agusta.

Mata kimanin 40 ne dai suka taru a gaban ofishin Ma’aikatar Ilimi ta Kasar a Kabul, suna kiraye kirayen neman ’yanci da aiki da kuma burodi, kafin a tarwatsa su da harbi a iska.

Kamfanin Dillancin Labaran Faransa (AFP) ya ruwaito cewa harbe-harben ta sa matan tserewa zuwa cikin shagunan da ke wurin, inda mayakan suka bi su, suka lakada musu duka.

Matan, dauke da kwalaye na kiraye-kirayen, “Adalaci, adalci, jahilci ya gundure mu,” kafin daga a watsa su taron nasu na neman ’yanci aiki da kuma damawa da su a siyasar kasar.

Masu zanga-zangar sun kuma daga kwalaye masu rubutn “15 ga Agusta bakar rana ce”.

A ranar da 15 ga watan Agusta, 2021 ne Taliban ta karbe ikon Afghanistan daga gwamnatin tsohon shugaban kasa, Ashraf Ghani, wanda ya tsare.