✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda mazajen Kano suke lakada wa matansu duka —Hisbah

Matsalar ta zama ruwan dare ta kuma kai intaha inda mazajen ke jikkata matan

Hukumar Hisba a Jihar Kano ta koka kan yawaitar korafe-korafen yadda mazaje ke lakada wa matansu dukan tsiya a Jihar.

Kwamandan Hukumar, Shaikh Muhammad Ibn Sina,  ya ce yanzu duka matan aure ya zama ruwan dare, inda a kullum ake kai wa hukumarsa irin wadannan korafe-korafe.

Sheikh Ibn Sina ya bayyana damuwa kan yadda matsalar ta kai intaha  a Jihar Kano, inda mazajen ke wuce gona da irin wajen lakada wa matansu dukan tsiya har su jikkata su.

“A kwanaki bakwai da suka gabata, mun karbi korafe-korafe har kashi 10 daga mata daban-daban wadanda mazajensu suka lakada wa duka wanda hakan ya nuna lamarin ya yi kamari,” inji Ibn Sina.

Kwamandan Hisban ya bayyana cewa hakan sabanin yadda ta kasance ne a lokutan baya ake samun korafe-korafen mata na daba wa mazajensu wuka a sassan jihar ne.

Ya ce amma a yanzu matsalar ta sauya fuska inda matan ke shan dukan tsiya a wurin mazajensu har ta kai sun raunatasu.

“Mafi alheri shi ne mutum ya zauna lafiya tare da iyalansa a madadin su bige da naushin juna,” inji Ibn Sina.

Ya hikaito ayoyi daga Al-Kur’ani mai girma da kuma koyarwar Annabi Muhammad (SAW) wadanda suka kwadwaitar da mazaje a kan nesantar kan dukan mata.