✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mazauna Potiskum sun koka kan lalacewar makabartu

Mazauna garin Potiskum da ke Karamar Hukumar Potiskum a Jihar Yobe, na ci gaba da bayyana damuwarsu dangane da lalacewar makabartun garin musamman a wannan…

Mazauna garin Potiskum da ke Karamar Hukumar Potiskum a Jihar Yobe, na ci gaba da bayyana damuwarsu dangane da lalacewar makabartun garin musamman a wannan lokaci na damina.

Wani mazaunin garin da lamarin ke ci masa tuwo a kwarya, Alhaji Gambo Mai Citta, ya bayyana cewa “yanayin makabartar Potiskum na zama abin damuwa ga mazauna garin a duk lokacin da aka yi ruwan sama.

“Saboda galibi a irin wannan lokaci gawarwakin wadanda suka mutu na bullutsowa yayin da wasu ke nutsewa cikin kasa,” a cewarsa.

Binciken da Aminiya ta yi ya nuna cewa, garin Potiskum na da makabartu akalla guda takwas da suka hada da makabartar SOCOL, Mamman Ali, Unguwan Jaji, Bayan Asibiti da Gishiwa Dabuwa.

Ragowar makarbatun su ne; Jigawa Mazaga, Nahuce da makarbatar Dumbulwa.

Bayanai sun ce mamakon ruwan sama da ya sauka a baya-bayan nan ya yi wa gidaje da gonaki barna, haka kuma makabartu sun yi fama da zaizayar kasa da ruftawar kaburbura.

Mazaunan sun yi kira ga gwamnati da ta jibinci lamarin cikin gaggawa, yayin da aka samu wadansu da suka bayar da gudummawar kasa don rufe wasu daga cikin kaburburan da gawarwakinsu suka bullutso waje.

“Babu shakka kabari shi ne wurin da kowa zai koma, idan muka yi watsi da gyara shi, wata rana za mu tsinci kanmu a wurin a cikin irin wannan yanayi mara kyau,” inji Mai Citta.

Kokarin da wakilinmu ya yi na jin ta bakin Shugaban Karamar Hukumar Potiskum bai haifar da da mai ido ba, kasancewar ya yi balaguro kuma bayan an tuntube shi ta wayar tarho bai amsa kiran ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.