✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mazauna Saudiyya ne kadai za su yi Hajji bana

Gwamnatin kasar Saudiyya ta takaita halartar aikin Hajji a bana zuwa wadanda ke zaune a kasar a halin yanzu kadai. Saudiyya ta ce mazauna wajen…

Gwamnatin kasar Saudiyya ta takaita halartar aikin Hajji a bana zuwa wadanda ke zaune a kasar a halin yanzu kadai.

Saudiyya ta ce mazauna wajen kasar ba za su halarci ibadar ba ta bana bana ba, kuma ta takaita adadin maniyyatan da za su yi aikin Hajjin da zai gudana a cikin wata mai zuwa ne domin kare yaduwar annobar coronavirus.

Ma’aikatar Kula da Harkokin Umarah da Aikin Hajji ta Saudiyya a cikin wata sanarwa a ranar Litinin ta ce ‘yan ko’ina a sassan duniya za su iya yin aikin Hajji, amma da sharadin ta kasance yanzu haka suna cikin kasar.

“Takaitaccen adadin mutane ‘yan kowace kasa da ke zaune cikin Saudiyya a yanzu haka za su iya yin aikin Hajji”, inji sanarwar, amma ba ta ambaci adadin alhazan da aka kayyade za su halarci ibadar ba.

Hakan na nufin mazauna wasu kasashe, ciki har da ’yan asalin Saudiyya da ke kasashen ketare ba sa daga cikin wadanda za su yi babbar ibadar a wannan shekarar ke nan.

Sanarwar ta kara da cewa mahukuntan kasar sun dauki matakin ne saboda kare alhazai da sauran jama’a daga barazanar kamuwa da cutar coronavirus a lokacin aikin Hajji.

“An yanke hukuncin hakan ne domin tabbatar da ganin an yi Hajji cikin aminci tare da kare lafiyar al’umma yadda ya kamata ta hanyar bin matakan kariya sau da kafa, da kuma bayar da tazara yadda ya dace”, inji ma’aikatar.

Ta kara da cewa “an dauki matakin ne sakamakon yadda ake kara samun hadarin yaduwar cutar a wuraren da jama’a ke taruwa.”

Hajji shi ne aikin ibada da ya fi tara al’ummar Musulmi daga ko’ina a fadin duniya a wuri daya a lokaci guda. A shekarar da ta gabata, alhazai miliyan 2.5 ne suka gudanar da aikin Hajji a bara.