✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mazauna sun firgita da ganin makwabci a cikin ’yan bindigar da suka kai musu hari

Mazauna sun gano cewa an yi zaman makwabtaka da dan bindigar a wani lokaci a baya.

Mazauna kauye Takakume da ke Karamar Hukumar Goronyon Jihar Sakkwato, sun kadu da ganin fuskar wani tsohon makwabcinsu a matsayin jagoran ’yan bindigar da suka kai musu hari.

A ranar Lahadi ce ’yan bindigar suka kai wa kauyen Takakume hari, inda bayan sun yi musayar wuta da wasu ’yan banga, karar kwana ta cimma jagoran ’yan bindigar wanda mazauna suka gano cewa an yi zaman makwabtaka da shi a wani lokaci a baya.

“Shi ne jagoran ’yan bindigar da suka kawo mana hari,” a cewar wani mazaunin kauyen da ya bukaci a sakaya sunansa.

Da yake zanta wa da manema labarai, shugaban Karamar Hukumar Goronyo, Malam Abdulwahab, ya ce ’yan bindigar sun kai harin ne da tsakar dare, inda suka yi ajalin wani mutum daya sannan suka yi awon gaba da wasu mutum shida.

“’Yan bangar da suka bi sahun ’yan binidgar sun samu nasarar kashe daya daga cikinsu, wanda daga bisani muka gano cewa shi ma wani tsohon mazaunin yankin ne da ke zama a gidan iyayensa.”

Shugaban Karamar Hukumar ya ce wannan hari shi ne na biyu da aka kaiwa kauyen a cikin ’yan kwanakin nan, inda har yanzu mutanen da aka dauke a harin na farko ba su kubuta ba.

Sai dai wata majiya kuma ta ce bakin cikin an kashe wa ’yan bindigar jagoransu ne ya sanya suka harbe mutanen da suka yi awon gaba da su.

Majiyar ta ce, ’yan bindigar sun harbe mutanen da suka sace, kuma da safiyar yau [Lahadi] muka kwaso gawawwakinsu aka yi musu janaiza.

Ya zuwa yanzu dai babu wani tabbaci dangane da wannan rahoton a hukumance, a yayin da gwamnati Jihar Sakkwato ko wata Hukumar Tsaro ba ta ce uffan a kai ba.