✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mazauna sun yi zanga-zanga kan matsalar tsaro a Kauran Namoda

A kwanakin baya bayan nan ’yan bindiga sun kara kaimi wajen kai hare-hare.

Mazauna sun yi zanga-zanga kan yawaitar kashe-kashen da ke aukuwa musamman a Karamar Hukumar Kaurar Namoda

Wadanda suka yi zanga-zangar a ranar Litinin domin nuna takaici a kan rashin tsaro, sun tare hanyar Gusau zuwa Kauran Namoda.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, masu zanga-zangar sun kasa kansu gida shida inda suka kona tayu a kan babbar hanyar mai tsawon kilomita sittin.

Masu zanga-zangar sun girke kawunansu a Sabon Garin Kauran Namoda, Mahadar Gwiwa, Fegin Magaji, Kuryar Madaro, Maguru, Kasuwar Daji da kuma Kyambarawa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, a kwanakin baya bayan nan ’yan bindiga sun kara kaimi wajen kai hare-hare musamman a yankunan karkara na Karamar Hukumar.

A Juma’ar da ta gabata ce wasu fusatattun mazauna yankin suka tafi da gawwakin mutanen da ’yan bindiga suka kashe har zuwa Fadar Sarkin Zurmi domin zayyana masa takaicinsu na matsalar tsaro da suke fuskanta.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun ce sun kai mataki na intaha kan yadda ’yan bindiga ke musu kisan kiyashi ba tare da hukumomin tsaro sun dauki wani mataki ba.

“Ana kashe mu kamar beraye, har zuwa yaushe za mu iya ci gaba da jure wannan abun takaici.

“Akwai yankin da ake shafe tsawon kwanaki uku ana kai musu hari ba tare da an dauki mataki ba saboda babu wanda ya damu da halin da suke ciki.

“Shin ko mu ba mutane bane, dole ne hukumomin da abin ya shafe su san halin da muke ciki domin daukar mataki, a cewar daya daga cikin masu zanga-zangar mai suna Aminu.

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, SP Muhammad Shehu, sai dai hakarta bata cimma ruwa ba yayin tattara wannan rahoto.