✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

MC Tagwaye ya angwance da Hauwa Uwais

Fitaccen mai barkwanci MC Tagwaye da ke yawan kwaiwayon maganganun Shugaba Muhammadu Buhari, ya zama angon. Ya auri diyar Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan…

Fitaccen mai barkwanci MC Tagwaye da ke yawan kwaiwayon maganganun Shugaba Muhammadu Buhari, ya zama angon.

Ya auri diyar Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Shirin Kyautata Rayuwar Jama’a, Maryam Uwais mai suna Hauwa.

A ranar Asabar MC Tagwaye, ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa an daura aurensu a ranar, kuma suna godiya ga jama’a.

Dan asalin jihar Anambra wanda asalin Sunansa Obinna Simon amma ya taso a Arewa, ya ce, “Ga masu tambaya…. mun yi aure cikin farin ciki yau… godiya”.