✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

MDD ta jinjina wa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya kan soke hukuncin kisa a kasarta

Yanzu dai kasar ita ce za ta kasance ta 24 a nahiyar Afirka da ta yi watsi da hukuncin

Hukumar Kiyaye Hakkin Da Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta yaba wa matakin da ’yan majalisar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya suka dauka na goge hukuncin kisa daga kundin dokokin kasar.

Rabon da a yanke hukuncin kisa a kasar dai tun a skekarar 1981, kuma a ranar Juma’ar da ta gabata, ’yan majalisar kasar sun amince da wata sabuwar doka a kasar da ta soke hukuncin kisa.

Shugabar hukumar, Michelle Bachelet, ta fada a cikin wata sanarwa ranar Laraba cewa, “Ina jinjina wa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya saboda yin fatali da hukuncin kisa, kumna ina kia ga Shugaba Faustin-Archange Touadera da ya rattaba hannu a kan dokar.

“Hukuncin kisa ya saba da ginshikan kare hakkin bil-adama na yanzu,” inji ta.

Tun a shekarar 2013 dai, kasar, wacce ita ce ta biyu wajen koma-baya a duniya inji Majalisar ta Dinkin Duniya take ta fama da yakin basasa.

Yanzu dai kasar ita ce za ta kasance ta 24 a nahiyar Afirka da ta yi watsi da hukuncin na kisa, inji Shugabar hukumar.

Ta kuma ce, “Yunkurin zai taimaka wa fafutukar da duniya take kokarin yi wajen yin watsi da tsarin baki daya, wanda kuma zai taka muhimmiyar rawa wajen inganta hakkin dan Adam.”