✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

MDD ta la’anci harin da aka kai wa sojojin wanzar da zaman lafiya Mali

Mayaka masu ikirarin jihadi sun shafe kusan awa daya suna luguden wuta da bindigogi da rokoki a kan jerin gwanon motocin.

Sakatare-Janar na Majalissar Dinkin Duniya, Antonio Guterak, ya yi Allah wadai da kazamin harin da aka kai wa jerin gwanon motocin jami’an tsaron samar da zaman lafiya a kusa da garin Kidal da ke Arewacin kasar Mali.

Mayaka masu ikirarin jihadi sun shafe kusan awa daya suna luguden wuta da bindigogi da rokoki a kan jerin gwanon motocin.

Hakan ya yi sanadiyar jikkata jami’an wanzar da zaman lafiya guda hudu ’yan kasar Jordan, wanda daya daga cikinsu ya rasu a asibiti sakamakon raunukan da suka samu.

Rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar Mali, ta ce karo na biyar ke nan da ake kai musu irin wannan hari a yankin Kidal.

Kakakin Majalisar Dinkin Duniya, Stéphane Dujarric, ya shaida wa manema labarai a birnin New York na kasar Amurka, cewa, “Harin na Kidal ya dawo da tunanin sarkakiya da Majalisar Dinkin Duniya da jami’anta wanzar da zaman lafiya suke ciki, da kuma irin barazanar da suke fuskanta a kullum.”

Da haka ya mika ta’aziyyar Majalisar Dinkin Duniya ga iyalan mamacin da kuma gwamnati da al’ummar kasar Jordan tare da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata.

Wakilin Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya a Mali, El Ghassim Wane, ya ce duk da kalubalen da jami’an tsaron wanzar da zaman lafiya suke fuskanta, suna samun goyon bayan al’umma da kuma gwamnatin kasar.