✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

MDD ta yi alkawarin taimaka wa Borno kawo karshen Boko Haram

A cewarsa, wannan wani muhimmin mataki ne domin samar da zaman lafiya a Najeriya, kasar da ta fi kowacce yawan jama’a a Afirka.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya (MDD), Antonio Guterres, ya yi alkawarin tallawa fa wajIhar Borno domin kawo karshen rikicin Boko Haram.

Da yake jawabi a lokacin ziyarar da ya kai Maiduguri ranar Talata, Guterres ya ce a shirye yake ya bayar da cikakken goyon baya ga kokarin kawo karshen rikicin masu tayar da kayar baya a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

A cewarsa, wannan wani muhimmin mataki ne na samar da zaman lafiya a Najeriya, kasar da ta fi kowacce yawan jama’a a nahiyar Afirka.

Guterres ya kuma bada tabbacin karin tallafin jinkai ga Jihar Borno, musamman domin sake gina muhallan mutanen da ke son komawa gidajensu cikin aminci da mutunci, bayan rikicin Boko Haram ya tilasta musu yin kaura zuwa sansanonin ’yan gudun hijira.

Bayan ya ziyarci wani sansanin ’yan gudun hijira da sansanin mayakan Boko da suka mika wuya da ke Gubio a Maiduguri, Mista Guterres ya bayyana cewa shirin mayar da ’yan gudun hijirar zuwa garuruwansu zai taimaka wajen samun zaman lafiya.

Da ya ke jawabi, Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya ce akalla mayakan Boko Haram 40,000 da iyalansu ne suka mika kansu tun bayan mutuwan shguaban kungiyar, Abubakar Shekau, a farkon shekarar 2021.

“Gwamnan ya shaida mini cewa yana bukatar samar da sabbin wurare domin tsugunar da da wadannan tsoffin ’yan ta’adda, kuma na yi alkawarin za mu ba da cikakken goyon bayan wannan aikin.

“Mafi kyawun abin da za mu iya yi domin zaman lafiya shi ne dawo da wadanda a lokacin da ake yanke kauna suka zama ’yan ta’adda amma a yanzu suna son zama ’yan kasa su kuma ba da gudummawa ga rayuwar ’yan uwansu,” inji Guterres.

A cewarsa, sake dawo da su na haifar da tashin hankali musamman a Maiduguri inda ’yan kasa suka suka yi fama da munanan hare-haren na Boko Haram sama da shekara goma.

Guterres, kafin ya bar jihar ta Borno sai da ya gana da wasu daga cikin tububbun mayakan na Boko Haram a sansanin da aka kebe su don canza musu tunani kafin mayar da su cikin jama’a.

Najeriya ta shafe fiye da shekara 10 tana fafatawa da kungiyar Boko Haram mai alaka da kungiyar IS a Yammacin Afirka, a rikicin da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da tilasta wa miliyoyi yin gudun hijira.