✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

MDD ta yi Allah wadai da mamayar Rasha a Ukraine

Kasashe biyar sun kada kuri'ar kin amincewa da kudirin yin Allah wadai da Rasha.

Kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya sun kada kuri’a da gagarumin rinjaye ta nuna kyama ga mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, inda suka nemi janyewarta nan take.

A yayin taron na gaggawa wanda ba kasafai ake irinsa ba, Rasha ta kare matakinta na mamayar makwabciyarta, tana musanta cewa ta aikata laifin yaki.

Haka kuma Rashan ta zargi kasashen yamma da matsa wa da kuma barazana ga kasashe kan su jefa kuri’ar amincewa da matakin, ba tare da ta bayar da wata shaida ba.

Kasashe 141 suka amince da kudirin daga cikin mambobin majalisar 193 a Babban Taron na Majalisar Dinkin Duniya

BBC ya ruwaito cewa, kasashje 35 suka kaurace wa kuri’ar, ciki har da Rasha da Indiya a taron na gaggawa wanda shi ne irinsa na farko tun 1997.

Rahoton ya kuma yi Allah-wadarai kan yadda Shugaba Putin na Rasha ya sanya dakarun nukiliya na kasarsa cikin shiri.

Daga cikin kasashen da suka goyi bayan Allah wadai da Rasha har da Najeriya da Nijar inda kuma aka samu kasashe biyar da suka kada kuri’ar kin amincewa da kudirin yin Allah wadai da ita.

Bai zo da mamaki ba da Belarus, babbar aminiyar Rasha ta bayyana adawa da kudirin. Syria ma babbar aminiyar Rasha ta ki amincewa da kudirin.

Haka ma Eritrea daga Afirka da Koriya Ta Arewa daga yankin Asiya da suka ki amincewa da kudirin yayin da China ta kauracewa zaman kada kuri’ar