Me Dokar Zabe ta ce kan canza ’yan takarar ‘wucin gadi’? | Aminiya

Me Dokar Zabe ta ce kan canza ’yan takarar ‘wucin gadi’?

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu
    Yakubu Liman

Wa’adin da Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) ta debar wa jam’iyyu na su mika sunayen ‘yan takararsu na kujerar Shugabancin Kasa da Mataimakansu ya kare a ranar Juma’a.

Jam’iyyun APC da LP sun mika sunaye na ‘wucin gadi’ na mataimakan masu takarar Shugabancin Kasa a jam’iyyunsu don kaucewa karewa wa’adi.

Dan takarar jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu dai, ya mika sunan Ibrahim Masari, wani dan siyasa daga Jihar Katsina a matsayin mataimakinsa ga Hukumar zabe amma na ‘wucin gadi’ ne.

Haka ma Peter Obi dan Takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Labour, shi ma ya mikawa hukumar sunan Doyin Okupe, shugaban yakin neman zabensa, a matsayin mataimakinsa, shi ma na ‘wucin gadi’.

Wannan dabara ta mika sunaye na ‘wucin gadi’ ga hukumar zabe, wata dabara ce da jam’iyyun da suka kasa tsayar da Mataimakin da zai mara wa dan takararsu baya a zaben Shugaban Kasa da ke tafe, gudun karya doka.

Sashe na 29 na (1) na Dokar Zabe da aka yi wa gyara ya tanadi cewa, jam’iyyun siyasa za su mika sunayen ‘yan takararsu ne a cikin kwana I80 kafin babban zabe na kasa.

Haka kuma sashe na 31 na dokar, ya ba jam’iyyun damar janye sunan dan takarar da suka mika, tare da sauya wani, a cikin kwana 90 kafin zabe.

Sai dai, a lokacin mika wa hukumar zabe sunayen, ba a ce mata na wucin gadi ba ne. Saboda babu wannan tanadin a doka.

Sai dai idan dan takarar ne da kansa ya janye, kuma a rubuce ga hukumar, kuma a cikin kwana 90 kafin zabe.

A yanzu, ‘yan Najeriya sun zuba ido don ganin wadanda aka mika sunayensu ga hukumar ko za ta yarda su mata cewa, sun janye don ra’a yin kansu nan da 12 ga watan Agusta a matsayin dama ta karshe.