✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Me ya sa akuya ta ‘jagoranci’ faretin nada Sarki Charles sarautar Ingila?

Me ya sa akuya ta ‘jagoranci’ tawagar nada Sarki Charles sarautar Ingila?

Yayin bikin nada sabon Sarkin Ingila, Charles III a hukumance a ranar Lahadi, bataliya ta uku ta dakarun masarautar kasar, ta yi tattaki a titunan Cardiff bisa jagorancin wata akuya.

Akuyar wacce ta fito daga tsatson da aka fi sani da Sheinkin ta hudu, ta janyo ce-ce-ku-ce musamman kan ma’anar hakan a al’adar kasar.

Bayanai daga kafafen yada labaran kasar na nuna cewa, akuyar guda ce daga tsoffin rukunin awakin da masarautar Ingilan ta ke raino tun a shekarar 1775.

Kafar yada labarai ta Grunge.com da ke kasar ta ce fiye da shekara 200 ke nan da masarautar kasar ta dauki nauyin rainon rukunin awakin da ake kira da Capra Hircus a wancan lokacin.

“Tarihi na nuna lamarin ya samo asali ne tun a shekarar 1775, a yakin Bunker Hill, inda wata akuya da ba a san daga inda ta bullo ba, ta shige gaban dakarun da ke rike da tutar kasar zuwa wata maboya.

“Daga nan ne gidan sarautar suka yanke shawarar rainonta, da zamowa a karkashin kulawarsu.

“Daga nan kuma suka amince akuyar na alamta samun nasara a kasar, inda aka fara daukar nauyinsu a fadin kasar,” inji kafar.

“Wani bayanin kuma da wasu kafafen suka fitar shi ne na yadda aka yi wa Sarauniyarr Ingila ta wancan lokacin wato Victoria kyautar ta, kuma bayan mutuwar akuyar, ta gabatar wa rundunar tsaron da wata ta yankin Kashmir.

“Daga nan ne ta ce magajiyar akuyar dole ne ta fito daga tsatson wadanda ake raina a gidan sarautar, wanda hakan ke nuna akuyar bangaren rundunar ce ba dabbar kiwo ba.

Ya zuwa yanzu dai Sarki Chares bai ce komai ba kan ko wannan al’ada za ta ci gaba yanzu da ya fara mulki.