✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Me ya sa El-Rufai bai yi ta’aziyyar Iyan Zazzau ba?

Kwana hudu da rasuwar Iyan Zazzau, gwamnan bai yi wa Masarautar ta'aziyya ba

Tun bayan rasuwar Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu, a ranar Juma’a 1 ga watan Janairun 2021, an yi kwana hudu ba tare da jin Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi wa Masarautar Zazzau ta’aziyya ba.

Yayin da mutane ke ta jajantawa tare da zuwa ko aikawa da sakonnin ta’aziyya ga Masarautar ta Zazzau, har zuwa safiyar Litinin ba a ji, kuma ba a ga, wata sanarwa daga Gwamnan da ke ta’aziyya game da rasuwar ba.

Jama’a dai na ta tsokaci a kan rashin jin ta’aziyyar Gwamna El-Rufai wanda ya fito daga Masarautar ta Zazzau, ko mai magana da yawunsa, game da rasuwar Iyan Zazzau, daya daga cikin ’ya’yan sarki a Masarautar.

Da farko wasu sun yi zaton a ranar Sadakar Uku (Lahadi), Gwamnan zai ziyarci Fadar Sarkin Zazzau domin yin ta’aziyyar sarakai biyu na Masarautar—Iyan Zazzau Alhaji Bashar Aminu da Talban Zazzau Alhaji Abdulkadir Pate—da aka sanar da rasuwarsu a rana guda. 

Mataimakiyar Gwamnan Kaduna, Hadiza Balarabe, a lokacin ta’aziyyar rasuwar Iyan Zazzau

Jinkirin da aka samu wajen jin duriyar gwamnan, musamman a shafukan sada zumunsa, duk da cewa yana wallafa abubuwa da dama a shafukansa a cikin kwanakin, ya daure wa jama’a kai.

Wani mai sharhi kan al’amura, Bashir Baba Muhammad, ya ce jinkirin da aka samu bai dace ba, musamman idan aka yi la’akari da matsayin mamacin da kuma muhimmancinsa a Masarautar.

Ko a ranar rasuwar, Gwamnan da kuma mai magana da yawunsa, Muyiwa Adeleke, sun fitar da sanarwar taya murnar shiga sabuwar shekara.

Bayan haka, El-Rufai ya yada wasu sakonnin sanarwa da aikace-aikacen gwamantinsa ta shafinsa na Twitter, har zuwa safiyar ranar Litinin.

Haka nan kuma babu wata sanarwa da aka gani a hukumance daga Ma’aiaktar Kananan Hukumomi da Masarauta ta Jihar Kaduna game da rasuwar.

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin Gwamnatin Jihar ta Kaduna game da lamarin, amma abin ya faskara.

A yayin da muke gab da kammala wannan labari, wakilinmu na Zariya ya shaida mana cewa Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Hadiza Balarabe Sabuwa, ta je Fadar Sarkin Zazzau a ranar domin gaisuwar ta’aziyya.

Har zuwa wannan lokaci dai babu wani bayani bayani cikakke game da abin da ya haddasa wa gwamnan jinkirin wurin mika taaziyyarsa ga Masarautar Zazzau kuma mahaifarsa.

An yi wa Talban Zazzau Sallar  Jana’iza aka kuma kai shi makwancinsa a ranar da ya rasu,  washegari da safe kuma aka yi Jana’izar Iyan Zazzau bayan an mayar da gawarsa Zariya daga Legas, inda ya rasu sakamkon rashin lafiya.