✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Me ya sa ’yan bindiga ke tursasa matan da suka kama auren su?’

Sabuwar dabi'ar dai yanzu na neman zama ruwan dare ga kungiyoyin ta'adda.

Wata mummunar al’ada da barazana dake tayar da hankulan iyaye da ’yan uwan ’yan mata wadanda tsautsayi ya ritsa da su suka fada hannun ’yan bindiga ko masu satar mutane ita ce barazanar yi musu fyade ko cewa za su aure su.

Sabuwar dabi’ar dai yanzu na neman zama ruwan dare ga kungiyoyin ’yan ta’adda kamar masu garkuwa da mutane ko ’yan bindiga da ’yan Boko Haram.

Ko a baya-bayan nan, wasu iyayen dalibai 29 na Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya dake Afaka a jihar Kaduna da suka rage a hannun ’yan bindiga sun koka kan haka, inda suka ce ’yan bindigar na musu barazanar aure dalibai matan da suke hannunsu.

Aminiya ta rawaito Sakataren Kungiyar Iyayen Daliban Kwalejin, Friday Sanni yana cewa, “’Yan bindigar sun ce za su aure ’yan matan daliban, kuma idan aka kai wani lokaci ko mun ba su kudaden ba za su yi amfani ba,” inji shi.

Suma daliban Makarantar ’Yan Mata ta Jangebe a jihar Zamfara da suka kubuta sun ce ’yan bindigar da suka sace su sun ba su lambobin waya tare da alkawarin zuwa gidajensu domin neman aurensu.

’Yan mata da dama da suka tattauna da Aminiya daga cikinsu sun ce ’yan bindigar sun shaida musu cewa suna son su da aure, sannan suka ba su lambobin wayarsu domin su kira su shaida musu ko sun amince da bukatar tasu ko kuma a’a.

Daya daga cikin ’yan matan ta shaida wa wakilinmu cewa ’yan bindigar sun kuma shawarce su da su yi watsi da karatunsu domin su samu su yi aure.

“Ana dab da za a sake mu, sai wasu daga ’yan bindagar sai suka zo suka fara nuna wasu daga cikinmu cewa suna so su aure mu in mun amince, wai bai kamata mu ci gaba da bata lokacinmu da sunan karatu ba,” inji ta.

Me ya sa ’yan ta’adda suka fi kai wa mata hari?

Aminiya ta tuntubi wata mai bincike da bibiyar ayyukan ‘yan ta’adda a Najeriya, Dokta Medinat Abdulazeez Malefakis, inda ta ce amfani ko cin zarafin mata da kungiyoyin masu tayar da kayar baya ke yi abun takaici ne da sosa rai matuka.

Ta ce, “Wani rahoton Kungiyar Human Rights Watch da aka wallafa a watan Nuwambar 2013 ya yi ikirarin cewa Boko Haram ta kai hari kan kauyuka sannan bayan ta kutsa gidajen da bai wa iyayen matan kudade da sunan sadakin yan matan, sai su dauke yan matan inda suke amfani da su domin biyan bukataun mayakansu.

“Ba ya ga yi wa matan fyade da cin zarafinsu ko muzguna musu, kungiyar na amfani da fyade wajen haifar magadan da za su ci gaba da yada manufofinsu na ikirarin Jihadi. Tsohon Gwamnan jihar Borno, Sanata Kashim Shettima ya nanata cewa shugabannin kungiyar da gayya suke yi wa matan da suka yi garkuwa da su ciki…”

“Jan hankalin da Boko Haram da ’yan bindiga suka yi sakamakon sace yan matan Chibok da na Dapchi da Jangebe misali babban abu ne. Shugabannin duniya sun yi ta wallafa sako kan maudu’in a shafukan sada zumunta; mutane a kasashe suna ta tofa albarkacin bakinsu.”

Tasirin amfani da mata da ’yan ta’adda ke yi

Yin hakan dai ya bunkasa Boko Haram ga shiga matakin kungiyoyin ta’addanci a duniya da suke amfani da mata wajen yada manufofinsu.

Malefakis ta ci gaba da cewa, yin barazanar aure ga mata ko cin zarafinsu ya taimaka sosai wajen kara matsa wa gwamnatin Najeriya lamba ta hanyar:

  1. Kunyata karfin Rundunar Sojin Kasar da suka gaza lalubo bakin zare kan yaki da ’yan ta’addar,
  2. Tilastawa Gwamnati zuwa teburin sulhu.
  3. Karbar kudade a matsayin fansa.
  4.  Yin amfani da matan tare da cin zarafinsu, da dai sauransu.