✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Me yake kawo cutar macijin ciki?

Macizan ciki ko tsutsar ciki suna daya daga cikin cututtukan da ake fama da su a duniya baki daya. Amma kowane yanki na duniya yana…

Macizan ciki ko tsutsar ciki suna daya daga cikin cututtukan da ake fama da su a duniya baki daya.

Amma kowane yanki na duniya yana da irin nasa macizan cikin da suka fi addabarsa sakamakon irin abincin da suke ci.

Macizan ciki suna totse albarkatun abincin da mukan ci, idan a yara ne kuma su hana su girma kamar yadda ya kamata.

Ana daukar wannan ciwo ne ta cin kwayayen wadannan macizai a nama walau na shanu ko tumaki ko aladu ko cin kwayayen da suke kasa a cin kasa da yara kan yi, ko shan ruwan da ya gurbata da wadannan kwayayen.

Idan kwayayen suka shiga ciki sai su kyankyashe su zama macizan ciki ko tsutsar ciki. Wasu kwayayen kuma a kasayar da su ta bahaya, idan wata dabba ko mutum ya ci a sake yada su.

Macizan ciki da aka fi gani a irin kasashenmu su ne Ascaris lumbricoides da yawancin yara kan kasayar (za a gan su dogaye kamar tana amma launinsu fari ko ruwan goro).

Sai Hookworm mai makalewa a ’ya’yan hanji na shan jini, sai kuma Guineaworm, mai kawo ciwon kurkunu.

Alamomin gane mai dauke da macijin ciki

Ba kasafai ciwon yake zuwa da alamomi ba. An fi ganin alamun a yara; alamun sun hada da yawan ciwon ciki da susar
duwawu saboda kwayayen sun fi zama a dubura, su sa wurin ya yi ta kaikayi.

Macijin Ascaris yakan yi girma sosai, ya toshe ’ya’yan hanji, ciki ya kumbura a kasa yin bahaya, a yi ta amai har sai an cire shi ta yin tiyata wato operation.

Shi kuma hookworm in ya fara shan jini za a ga yaro yana yin fari yana ramewa, ba ya girma kamar sauran ’yan uwansa duk da cewa yana cin abinci sosai.

Ita kuma tsutsar Guineaworm mai kawo kurkunu, kafa take saukowa ta huda wajen agara ko idon sawu ta fara fitowa (za a gan ta fara kuma doguwa), wurin kuma ya zama gyambo. Idan ta fara fitowa sai ta yi kwanaki kan ta gama fitowa.

Don haka akan samu kara a nannade ta a jiki a rika janyo ta a hankali ba lokaci guda ba don kada ta tsinke, don in ta tsinke sai an yi tiyata an ciro ta.

Hanyoyin kariya daga wannan ciwo

• A wanke nama kuma a tafasa sosai don qwayayen da dabba ke dauke da su su mutu, musamman kayan ciki

• A irin wannan lokaci na bayan Sallah da aka ci nama iri-iri aka gyatse, yana da kyau kowa ya nemi maganin tsutsar ciki ya sha domin kariya

• A rika tacewa da kuma barin ruwan da aka diba a rafi ko rijiya mara zurfi ya
kwanta, sannan in da hali a dafa kafin a sha.

• A rika wanke hannu da sabulu bayan an yi bahaya saboda kwayayen kan zauna a hannaye

• Idan yaro ko wani babba ya yi bayan gida mai dauke da macijin ciki to ya je asibiti a ba shi maganin kashe sauran kwayayen da ke cikinsa

• A rika kula da yara sosai kada su ci kasa, a kuma rika yawan wanke musu hannuwa da sabulu duk lokacin da suka je wasa suka dawo

• A kai mai ciwon kurkunu asibiti mafi kusa ko a sanar da hukuma mafi kusa don daukar mataki

• A guji bahaya a kusa da magudanun ruwa ko gonaki ko fadamu saboda gudun yada kwayayen

• Hukumomi musamman na kananan hukumomi su ci gaba da samar da ruwa mai tsabta kamar rijiyoyin burtsatse ga jama’arsu

• Hukumomi su fito da tsarin ba wa yaran makarantun firamare magungunan kashe macizan ciki akalla sau daya a zangon karatu.