✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Me zai faru bayan rasuwar dan takarar NNPP dab da zabe?

Abin da dokar Najeriya ta ce kan rasuwar dan takara gabanin gudanar da babban zabe

Rasuwar dan takarar Jam’iyyar NNPP na Majalisar Tarayya na mazabar Wudil da Garko, Kamilu Ado Isa kasa, mako guda kafin zaben 2023, ta sa hankali ya koma kan yadda za ta kaya da takarar.

Isa wanda tsohon Kwantrola-Janar ne na Hukumar Sibil Difens,  ya rasu ne bayan takaitacciyar jinya.

Baya ga dan takarar NNPP, akwai na APC a Kwara Olawoyin Mogaji, da ke zawarcin kujerar majalisar jiha karo na biyu, inda shi ma zaben cike gurbi da jam’iyyar ta gudanar ta maye gurbinsa da dan uwansa Oba Mogaji.

Haka kuma a baya-bayan nan ma dan takarar Gwamnan a PDP Abia Uche Ikonne ya rasu, kuma jam’iyyar ta maye grbinsa da tsohon shugaban ma’aikatan  jihar, Okezie Ikpeazu.

To sai dai bambamcin wadannan rashe-rashe da ta Isa shi ne, karancin lokacin da NNPP ke da shi na maye gurbinsa.

Aminiya ta tattauna da fitaccen lauya a Kano, Barista Abba Hikima, kan tanadin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya yi idan irin haka ta faru.

Ya bayyana cewa “Kundin dokar Zabe ta 2022 ta hararo irin wannan yanayin kuma ya samar da amsa a sashi na 34.

“Karkashin sashin, idan aka samu dan takara ya rasu, ko janye wa daga takara gabanin babban zabe, jam’iyyarsa na da damar yin sabon zaben cikin gida a kwana 14 wato sati biyu ke nan.

“Haka kuma hanyoyin da za a gudanar da zaben cikin gida sun hada da zaben kato bayan kato, ko na daliget, ko sulhu.

“Abu mafi muhimmanci dai a samar da dan takarar, kuma wannan abu ne da za a iya yin sa a kwana daya ma idan jam’iyya ta yi ra’ayi.”

Sai uwar jam’iyya ta sanar da INEC  —NNPP Kano

Sunusi Bature Dawakin Tofa shi ne Kakakin dan takarar Gwamnan Kano na jamiyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf, ya kuma ce tun bayan kammala duk abin da ya kamata na alhinin rasuwar dan takarar suka sanar da uwar jam’iyya halin da ake ciki don daukar mataki na gaba.

“Mun rubuta wa uwar jam’iyya abu mara dadi da ya faru, kuma muna sa ran a yau din nan in Allah Ya yarda za ta rubuta wa INEC a hukumance ta sanar da ita abin da ya faru, kuma muna sa ran hukumar za ta ba mu damar maye gurbinsa kafin a shiga zabe.

“Kuma abin da muka sani shi ne cikin yardar Allah ba za a shiga wannan zabe ba sai da dan takarar NNPP.

“Ta yiwu INEC ta yanke hukunci cewa a dage iyakacin wannan zaben na kujerar, ko kuma ta ba mu dama mu fito da sabon dan takara a satin nan kan zabe,” in ji shi.

Bisa dokar zaben dai, idan har jam’iyyar NNPP ta gaza fitar da dan takarar da zai maye gurbin margayin, sauran abokan karawarsa na APC Muhammad Ali Wudil da Ahmad Rufai Idris na PDP, za su dakaci sabuwar ranar zaben kujerar da INEC za ta sanya.