✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mece ce makomar siyasar Kwankwaso bayan ficewa daga PDP?

Shin tsohon Gwamnan na Jihar Kano ya dauki layi mara bullewa?

Tun bayan da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya fice daga PDP tare da komawa NNPP, wasu ke ganin cewar ya dauki layi mara bullewa.

Sai dai, siyasa, kamar yadda wasu ke cewa, lissafi ce tamkar yadda gwanaye a harkar kwallon kafa ke murzata yadda suke so, haka ita ma wani lokacin take.

Sanata Kwankwaso ya fice daga PDP a farkon satin da muke bankwana da shi, kuma ’yan gaban goshinsa, wato Injiniya Abba Kabir Yusif (Abba Gida-gida) da Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, su ma tuni suka sauya sheka zuwa sabuwar jam’iyyar siyasar mai alamar kayan marmari, wato NNPP.

Wasu masu sharhi a al’amuran siyasa na ganin son yin takarar Shugaban Kasa ce ta sa Sanata Kwankwaso da mukarrabansa sauya shekar zuwa jam’iyya mai kayan marmari. Wanda a tunaninsu hakan na iya kai shi ya baro, duba da irin tarin kalubalen da ke gabansa musamman, wato manyan jam’iyyun na APC da PDP.

A wani kaulin kuma, wasu na ganin cewar Sanata Kwankwaso ba burinsa zama Shugaban Kasar Najeriya a yanzu bane, a’a sai dai neman ya kafa gwamnati a Jihar Kano.

‘Yanzu an bar siyasar akida’

Farfesa Kamilu Sani Fagge, masanin Kimiyyar Siyasa ne a Jami’ar Bayero da ke Kano, ya bayyana sauyin shekar da ’yan siyasa ke yi a matsayin rashin akida ta siyasa wanda kuma yake kawo wa siyasar kasar nan tarnaki.

“Wannan yana nuna cewa a yanzu an bar siyasar akida, siyasa ta zama ta kasuwar bukata. Duk wanda bai samu biyan bukatarsa a jam’iyyar da yake ba, sai ya tattara kayansa ya koma wata.

“Wannan ya sa siyasar kasar nan ba ta ci gaba,” inji shi.

Al’amura da dama sun faru, wanda suka sa tsohon Gwamnan ya dinga sauya sheka daga nan zuwa can.

Da fari, bayan yin tafiyar maja ta APC a 2015, Kwankwaso ya koka kan yadda aka mayar da shi saniyar-ware, inda ake gudanar da al’amura a jam’iyya mai mulki APC ba tare da sanya shi a sahun gaba na wanda suka hidimtawa jam’iyyar wajen lashe zabe ba.

Matsaloli da dama suka taru suka sanya Kwankwaso ficewa daga APC zuwa PDP.

Bayan gaza kafa gwamnati a 2019 da Kwankwaso da mukarrabansa suka yi a Jihar Kano, matsaloli sun far masa inda ya gaza samun mukamai hatta a zaben shiyyar Arewa maso Yamma da aka gudanar na jam’iyyar PDP a baya.

Hakan ya haifar da rashin jituwa tsakanin tsohon Gwamnan na Kano da Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, inda kowane bangare ke zargin dayan na iya yi masa bita-da-kulli.

Har wa yau, jam’iyyar ta PDP a Kano ta samu rarrabuwar kai, inda wasu suka bijirewa jagoran na darikar Kwankwasiyya, musamman irin su Aminu Wali da Dokta Yunusa Adamu Dan Gwani.

Bayan abubuwa sun yi tsami, Sanata Kwankwaso ya kafa wata sabuwar tafiyar siyasa da aka yi wa lakabi da The Nigeria Movement, wato TNM.

Wannan tafiya ta kunshi manyan ’yan siyasa da ke fadin Najeriya, amma wasu na da ra’ayin cewar Sanata Kwankwaso shi kadai ne mai kwari a cikin tafiyar, kuma da yawan wanda suka shiga tafiyar za su kasance ‘yan amshin shata ne.

Za su iya ba da mamaki a 2023 – Masani

Dokta Saidu Ahmad Dukawa masanin siyasa ne a Jami’ar Bayero ta Kano; ya yi wa Aminiya fashin-baki kan irin rawar da Sanata Kwankwaso da kuma tafiyar TNM za su iya takawa a zaben 2023 mai zuwa.

“To babbar rawar da kungiyar TNM ta su [tsohon Sanata Rabi’u Musa] Kwankwaso za ta iya takawa nan da zabukan 2023, ita ce ta kokarin samar da maja – ya zamana an sami wasu kananan jam’iyyun da dama sun hadu sun narke sun hada wata maja shigen wacce aka yi a APC.

“To idan suka samu yin haka kuma ’yan kasa suka amince musu, to za su iya girgiza jam’iyya mai mulki ta APC, kuma watakila ma su yi nasarar karbar shugabanci.

“Amma wannan ya danganta da irin dan takarar da suka tsayar da karbuwarsa da kuma wadanda PDP da APC za su tsayar da tasu karbuwar.

“To idan suka tsai da duk wanda ya fi wadanda APC ko PDP za su tsayar, to za su iya ba da mamaki a 2023,” cewar Dukawa.

Amma ya yi karin haske cewar, kaf cikin tafiyar TNM babu wani dan siyasa da ya kai nauyin Kwankwaso, don haka wasu ke ganin da wuya ya iya kai wa gaci shi kadai, matukar ba wasu ne suka mara masa baya ba.

Wadansu na ganin shigar Sanata Rabi’u Kwankwaso da Injiniya Abba Kabir Jam’iyyar NNPP za ta ba jam’iyyar karfin da ake ganin za ta zama barazana ga Jam’iyyar APC a Kano.

Ba mu girgiza ba – APC

Sai dai Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC a Jihar Kano, Ahmad S. Aruwa, ya ce Jam’iyyar APC ba ta girgiza da jin wannan labari ba.

“Ana ta surutu wai Abba da Kwankwaso sun shiga Jam’iyyar NNPP, wannan ba barazana ba ce gare mu domin bikin Magaji ba ya hana na Magajiya,” inji shi.

A satin da ya wuce ne, jam’iyyar ta NNPP ta gudanar da babban taronta na kasa a Babban Birnin Tarayya Abuja, inda ta nada Sanata Kwankwaso a matsayin jagoranta na kasa.

Ya zuwa yanzu dai, babban zaben 2023 na kara matsowa, kuma kowace jam’iyya musamman APC da PDP na kokarin fito da dan takarar da zai jagorance ta a babban zaben.

Daga daya hannun kuma, NNPP ta su Sanata Kwankwaso na matsa lamba ga wadannan jam’iyyun biyu, sai dai ayar tambaya a nan ita ce, shin Sanata Kwankwaso zai iya darewa kujerar Shugabancin Kasar nan a 2023 a NNPP?