✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Medinat Abdulazeez Malefakis: Gwanar yaki da ta’addanci

Dokta Malefakis ce ’yar Arewa mafi kuruciya da ta yi digiri na uku (PhD)

In dai batun nazari a kan tsaro a duniya ne, musamman ma yaki da ta’addanci da tashe-tashen hankula  da samar da tsaro da kuma matsalar ’yan gudun hijira a yankin Tafkin Chadi, to Dokta Medinat Abdulazeez Malefakis tana cikin masana na gaba-gaba.

A yanzu haka tana tare da Jami’ar ETH dake Zurich, Switzerland, inda take gudanar da bincike a kan yadda ake amfani da soshiyal midiya (kafofin sadarwa na zamani) don rura wutar rikici ko samar da zaman lafiya.

A lokaci guda kuma mamba ce ta wani kwamiti mai zaman kansa a gidauniyar Global Community Engagement and Resilience Fund (GCERF) mai tallafa wa mutanen da munanan tashe-tashen hankula suka shafa.

Ita ce take tantance sahihancin bukatun neman taimakon da ake tura wa asusun gidauniyar ta GCERF mai bayar da tallafi don yakar tsattsauran ra’ayin gani-kashe-ni.

Bugu da kari, Medinat Abdulazeez Malefakis ce mai bayar da shawara game da batutuwan da suka shafi Najeriya a Asusun Tallafa wa Wadanda Suka Tsira daga Munanan Tashe-tashen Hankula a Duniya (Global Survivors Fund, GSF) wanda ke Geneva.

Wani abin burgewa game da Tauraruwar kuma shi ne jagorantar kungiyar farar hula ta Fundamental Impact Project mai tallafa wa mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da muhallinsu ta hanyar koya musu dabarun sauya rayuwarsu.

’Yar Arewa mai PhD mafi kuruciya

Medinat ta yi digirinta na farko ne a fannin Tarihi a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, sannan ta yi na biyu a fannin Nazarin Huldodin Kasa-da-Kasa a Makarantar Horar da Hafsoshin Soji ta Najeriya (NDA).

Ta fara karatun digiri na uku (PhD) a fannin na Nazarin Huldodin Kasa-da-Kasa a NDA, sai ta samu gurbin karo karatu a Jami’ar Zurich, don haka ta yi adabo da mutanen Zariya.

A lokacin da ta kammala karatun digiri na uku, an ce tana cikin matan Arewa mafiya kuruciya da suka yi digirgir – a lokacin tana da shekara 27 da haihuwa zuwa 28.

Haka ma lokacin da ta kammala karatunta na digirin farko da na biyu, duk ita ce mafi hazaka a cikin daliban da ta yi karatu tare da su.

Bayan ta yi digirin digirgir dai Dokta Malefakis ta yi aiki da Cibiyar Max Planck da ke Jamus a matsayin Karamar Mai Bincike, sannan ta zama Babbar Mai Bincike a Cibiyar Nazarin Dabarun Samar da Zaman Lafiya ta Amurka (USIP).

Iyali

Ta kuma yi aiki da Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Norway da ke Geneva.

Haka kuma Dokta Malefakis ta taba aiki da Hukumar Raya Kasashe ta majalisar Dinkin Duniya (UNDP), da kungiyar tsaro ta NATO da Cibiyar Zaman Lafiya ta Toda da ke Japan, da sauransu.

Medinat Malefakis tana da aure, kuma Allah Ya albarkace ta da ’ya’ya.

Ta kuma yi amanna cewa ta kai inda take yanzu ne saboda kasancewarta Musulma ’yar Najeriya.