✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mene ne matsayin azumin Sitta Shawwal a Mazhabar Malikiyya (2)

Alhamdulillah, a makon jiya ne muka fara gabatar da wannan rubutu wanda fahimtar malaman Mazhabar Malikiyya ce a kan azumin Sitta Shawwal a wani yunkuri…

Alhamdulillah, a makon jiya ne muka fara gabatar da wannan rubutu wanda fahimtar malaman Mazhabar Malikiyya ce a kan azumin Sitta Shawwal a wani yunkuri na warware shubuhar da ake samu a tsakanin mabiya mazhabar a nan Najeriya.

Yayin da wadansu ke kokarin haramta azumin wadansu kuma nema suke yi su mayar da shi wajibi.

Muna fata da wannan dan rubutu da muka ciro daga shafin Cibiyar Imam Malik ta Intanet (Markazu Imam Malik) za a kawar da wannan takaddama.

1. Na ce ya dace a gabatar da biyan azumi ban ce ya wajaba daga farko ba.

Ya inganta a yi Sitta Shawwal kafin biyan azumin Ramadan; kalmar ya dace tana nufin wannan ne mafi kyau kuma wannan ne abin da Sheikh Bin Tahir ya ambata a fatawarsa, inda ya ce: “Ana gabatar da biya daga farko bisa aiki da ka’idar ‘Wajibi ne mafi dacewa da gabatarwa’.”

2. Na yi magana ce kan mas’alar a hali na bai-daya da aka saba, yayin da shi kuma ya yi ishara da hali na kebe yana mai togewa, ita ce rashin ikon biyan azumin da Sitta Shawwal a cikin watan, sai ya bayyana a wannan hali da cewar gabatar da Sitta Shawwal da ake tsoron kubucewarsa.

A nan akwai bambanci a tsakanin halayen biyu. Mafi dacewa gabatar da biyan Ramadan a kan azumin nafila.

Kuma a cikin halin gazawa da rashin ikon haka sai aka yi rahusa kan a yi azumin Sitta Shawwal kafin biyan Ramadan don kada su kubuce.

Fatawar Al-Jaza’iri

Fatawar Sheikh Abu Sharfuddin Al-Jaza’iri.

Shin azumin Sitta Shawwal makaruhi ne a wurin Malikiyya? Kuma mene ne hukuncin hada su a niyya daya da azumin ramuwa?

Amsa: Ga Allah muke neman dacewa; da sunan Allah Mai rahama Mai jinkai.

Godiya ta tabbata ga Allah Makadaici. Tsira da Amincin Allah su tabbata ga wanda babu wani Annabi a bayansa.

Bayan haka, lallai Allah Madaukaki Ya shar’anta a tare da kowace farilla wasu nafilfili don karfafa abin da zai iya aukuwa na nakasu ko sakaci.

Kuma daga cikin abin da Ya shar’anta a harshen AnnabinSa (SAW) akwai azumin Sitta Shawwal.

Imam Muslim da wadansu sun ruwaito cewa lallai Annabi (SAW) ya ce: “Wanda ya azumci Ramadan sannan ya bi shi da shida a Shawwal kamar ya yi azumin shekara ne.”

Sitta Shawwal a Shari’a

Don haka azumtar Sitta Shawwal shari’antacce ne kuma mandubi, sai dai Imam Malik (Allah Ya yi masa rahama) ya karhanta haka ne saboda wata illa da ya bayyana a cikin Muwadda.

Ya ce: “Lallai ni ban ga wani daga cikin ma’abota ilimi da fikihu na azumtarsu ba, kuma hakan bai riske ni daga wani daga cikin magabata ba.

“Kuma ma’abota ilimi suna karhanta haka suna tsoron kasancewarsa bidi’a da kuma riskar da Ramadan ga abin da ba ya cikinsa daga jahilai da masu jafa’i” (Muwadda, Juz’i na 1 shafi na 310).

Alkali Iyal ya ce, “Akwai yiwuwar Malik ya karhanta azumin ne a kan wannan dalili: mutum ya yi ittikadi a kan farilla ne.

“Amma wanda ya azumce su bisa fuskar da Annabi (SAW) yake nufi hakan ya halasta”( Ikmalul Mu’allim na Alkali Iyal, Mujalladi na 4 shafi na 139).

Amma fadin masu da’awar cewa Hadisin bai riski Malik ba, da’awa ce marar hujja, domin malaman Hadisi shida sun ruwaito Hadisin, kuma misalin wannan ba zai buya ga Malik ba, wanda shi ne babban malamin Madina kuma Shugaban Masu Hadisi “Ba zai jahilci wani abu daga wannan ba” (Al-Istizkar na Ibn Abdulbarri, mujalladi na 3 shafi na 380).

Amma hada su a niyya tare da niyya daya yana shiga abin da Fukaha’u suke kira da Tashrik (hadawa) a tsakanin ibadoji biyu da niyya daya.

A nan Malikiyya ba su amince da Tashrikin (hada) ramuwar azumi da azumin Sitta Shawwal bisa niyya daya ba, saboda hakan abin kyama ne a wurinsu don illar da ta gabata.

Amma sun amince da hadawar a Juz’iyyati na daban: daga ciki akwai hada azumin ramuwa da azumin Ashura ko Arfa ko hada alwala da wanka ko wankan Juma’a da na Janaba ko Tahiyyatul Masjid da Azhar ko raka’o’in Ihrami ko raka’o’in Dawafi tare da farilla…

A falala abin da ya fi shi ne:

1) Falala mai daraja ta daya: Mutum ya rama azumi yana mai gabatar da shi a kan Sitta Shawwal, kususan ga wanda ya yi niyyar ya biya a watan Shawwal, domin falalar Sitta Shawwal ba ta samuwa – bisa zahirin Hadisin da ya gabata – sai ga wanda ya biya abin da ke kansa na ranakun Ramadan da ya sha bisa uzuri.

A cikin wannan akwai fa’idoji biyu: Haduwar malamai a kan haka da kuma guje wa sabani.

2). Daraja ta biyu: Ya azumci Sitta Shawwal sannan ya bi su da ramuwar Ramadan a lokacin da ya so, kususan ga wanda ya yi niyyar ya jinkirta ramuwar zuwa bayan Shawwal.

Sabanin malamai

Kuma kan haka malamai sun yi sabani:

Hanafiyya sun halasta hakan kai-tsaye saboda lokacin yin Sitta Shawwal ya fi karanci a kan lokacin biya wanda shi ne shekara gaba dayanta. Don haka suka gabatar da wanda ya fi kunci a kan mai yalwa.

Hambaliyya sun haramta azumin nafila kafin biyan na Ramadan yanke.

Suka ce bashin Allah ya fi cancanta a biya. Kuma farilla ce ta fi dacewa a fara da ita a kan nafila.

Wannan a fili akwai tsanantawa a ciki, domin haramci yana bukatar dalili kuma a nan babu dalilin da za a dogara da shi.

Su kuwa Malikiyya da Shafi’iyya sun tafi ne a kan halalci tare da karhanci saboda abin da yake jerantuwa na shagala da tadawwu’i a kan ramuwar wajen jinkirta wajibi.

Kuma mafi alherin al’amari tsaka-tsakinsa – “Kamar haka Muka sanya ku al’umma matsakaiciya.”

Dalilin halascin abin da ya tabbata daga A’isha (RA) ta ce: “Yakan kasance a kaina akwai ramuwar azumin Ramadan, amma ban iya biya – sai a cikin Sha’aban.”

Wannan saboda shagaltuwa da Annabi (SAW). Buhari da Muslim suka ruwaito.

3). Daraja ta uku: Ya hada tsakanin ramuwar da Sitta Shawwal da niyya daya.

Wannan yana cikin hukuncin hada tsakanin nafila da farilla, kamar Sallar Tahiyyatul Masjid da Azahar ko tsakanin babba da karami kamar alwala tare da wanka.

Hakika malamai sun hadu a kan halascin haka a Wasa’il kamar alwala da wanka, ko wankan Juma’a tare da na Janaba, kamar yadda suka hadu a kan halascinsa a mas’ala daya ta Makasid, shi ne Kirani a Hajji, inda ake hada Umarah da Hajji da niyya guda.

Kuma da shi Annabi (SAW) ya yi Hajji a bisa magana mafi rinjaye. Sai suka yi sabani a bayan wannan cikin Makasid, misali hada Tahiyyatul Masjid da Azahar ko ramuwar azumi tare da Ashura.

Mun tsakuro wannan ne daga fatawar Sheikh Abdullahi Bin Tahir As-Susiy ta ran Juma’a 5 ga Shawwal, 1438 Bayan Hijira daidai da 30 /6/2017 Miladiyya.

Kayyade karhanci

Da wannan za mu ga cewa malaman Mazhabar Malikiyya da suka biyo baya sun kayyade karhancin yin azumin Sitta Shawwal da aka ruwaito Imam Malik (Allah Ya yi masa rahama) ya fadi a kan kada a sadar da su da azumin Ramadan wato nan take da an yi Sallar Idi.

Kuma kada mutumin da ake koyi da shi – shugaba ko babban malami – ya bayyana azumin.

Kuma kada ya kudurta cewa sunnoninsu ga Ramadan kamar sunnonin jeranta Ba’adiyya a Sallah ne.

Kuma kada mutum ya yi azumin dodar kwana shida a jere.

Suka ce idan aka aikata wadancan ne azumin ke zama makaruhi, amma in aka kiyaye su to azumin ya zama mustahabbi.

Allah Ya datar da mu ga abin da yake mafi daidai kuma Ya shiryar da mu ga tafarki madaidaici.