✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mesa mafi girma a duniya mai tsawon kafa 18 ta shiga hannu

Mesa tana da nauyin kilo 98 da tsawon kafa 18

Wadansu ’ya’yan kungiyar Masana Kimiyyar Halittu sun kama wata macijiya jinsin mesa da aka kiyasta ita ce mafi girma da aka taba kamawa a Jihar Florida da ke Amurka.

Mesa tana da nauyin kilo 98 da tsawon kafa 18 (daidai da mita 5), inji jami’a masu kula halittun cikin ruwa a Kudu maso Yamma na Florida a wata sanarwa da suka fitar.

Ayarin sun yi amfani da na’urar tatsar bayanai ta rediyo da aka dasa a jikin macijiyar don nazarin motsinta da halayen kiwonta da wuraren zama, inji Masanin Halittun Daji kuma Manajan Shirin Kimiyyar Muhalli na halittun ruwa, Mista Ian Bartoszek.

“Yaya ake samun allura a cikin tarin ciyayi? Kuna iya amfani da mayen karfe, kuma haka nan macizanmu maza suna sha’awar manyan macizai mata da ke kewaye,” inji Bartoszek.

Ayarin sun yi amfani da wani maciji mai suna Dionysus – a wani yanki na yammacin Eberglades.

“Mun san yana wurin saboda wani dalili, kuma jami’an sun same shi da macijiya mafi girma da muka taba gani a yau,” inji shi.

Masanin halittu, Ian Easterling da wani kwararre mai suna Kyle Findley ne suka taimaka wajen kama macijiyar kuma suka dauke ta a cikin kejin itace zuwa babbar motar.

Har ila yau, an samu wani kofato a cikin gurbin narkar da abinci na macijiyar, ma’ana babbar macijiyar ta ci wata babbar dabba a matsayin abincinta na karshe.