✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda Rasuwar Pele Ta Girgiza Duniyar Kwallon Kafa

Duniyar kwallon kafa ta girgiza da rasuwar fitaccen dan wasan kwallon kafa na duniya dan kasar Brazil, Edson Arantes do Nascimento wanda aka fi sani…

Duniyar kwallon kafa ta girgiza da rasuwar fitaccen dan wasan kwallon kafa na duniya dan kasar Brazil, Edson Arantes do Nascimento wanda aka fi sani da Pele.

Fitattun ’yan kwallon kafa na duniya, irinsu Lionel Messi na Ajentina da Cristiano Ronaldo na Portugal da Kullum Mbappe da tsohon dan wasan Najeriya, Kanu Nwanko na daga cikin wadanda suka fara mika ta’aziyyrasu.

Bayan sanar da rasuwar Pele da ’yarsa da manajansa suka yi a ranar Alhamis, Lionel Messi, ya wallafa hotonsa da Pele a shafinsa na Instagram cewa, “Huta lafiya Pele.”

A nasa bangaren, Cristiano Ronaldo, ya sanya hotonsa da Pele, sannan ya ce, “Na kadu matuka da mutuwar Sarki Pele. Ba zan taba mantawa ba da shi a rayuwata. Muna godiya da murmushin da ka sanya a fuskokinmu.”

Messi da Ronaldo dai su ne manyan ’yan wasan duniya da ake takaddama kan wanda ya fi zama gwarzo a cikinsu — bayan Pele.

Kyllian Mbappe na Faransa, wanda ya ja hankalin masoya kwallo a Gasar Cin Kofin Duniya ta Qatar 2022, ya wallafa hotonsa tare da Pele a Twitter yana cewa, “Sarkin Kwallon Kafa ya tafi, amma abubuwan da ya yi ba za a taba mantawa ba.”

Neymar Junior, ya wa wallafa a shafinsa na Instagram cewa, “Pele ne ya mayar da kwallon kafa adabi da nishadi …ya tafi, amma suddabarunsa na nan.”

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce, Pele, “Muna godiya bisa yadda ka kayatar da masoyan kwallon kafa a faɗin duniya.”

Kafar wasanni ta ESPN ta ce, “Gwarzon dan wasan kasar Brazil Pele ya rasu yana da shekara 82.

“Shi ne asalin gagara-badau da babu kamarsa.

“Miliyiyon mutane za su yi kewarsa.”