✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Messi ya bar Barcelona bayan shekara 21

Messi ba zai ci gaba da zama a kungiyar ba saboda matsin tattalin arziki.

Lionel Messi ya bar Barcelona bayan shafe shekara 21 yana murza leda a kungiyar.

Wata sanarwa da kungiyar ta fitar a yammacin Alhamis, ta ce sun cimma yarjejeniyar raba gari da fitaccen dan wasan sakamakon matsalolin kudi da suka yi mata kaka-gida a yanzu.

A kan haka ne Barcelona da wakilan dan wasan ke takaicin kasa kulla yarjejeniyar ci gaba da aiki tare kamar yadda kungiyar ta sanar a shafinta.

Barcelona ta ce da zuciya daya tana mika godiya ga dan wasan musamman kan irin gudunmuwar da bayar na habaka kungiyar, inda take masa fatan alheri kan abin da gabansa za ta kasance.

Messi mai shekara 34 bai da yarjejeniya da wata kungiya tun bayan karewar kwantaraginsa da Barcelona a karshen watan Yuni.