Messi ya kwanta rashin lafiya bayan lashe Ballon d’Or | Aminiya

Messi ya kwanta rashin lafiya bayan lashe Ballon d’Or

Lionel Messi
Lionel Messi
    Abubakar Muhammad Usman

Gwarzon dan kwallon kafa na duniya da ke taka lada a PSG, Lionel Messi ya kwanta rashin lafiya bayan lashe kambun Ballon d’Or a makon nan.

Kungiyarsa ta PSG ta bayyana cewar dan wasan na fama da ciwon ciki tun bayan kammala bikin bayar da kyautar gwarzon dan wasa ta Ballon d’Or da aka gudanar a kasae Faransa.

Sai dai sanawar da PSG ta fitar a yammacin Laraba ta ce tana fatan Messi zai warware kafin karawarta da kungiyar Lens a gasar Ligue 1, a ranar Asabar.

Dan wasan dan na kasar Ajantina mai shekara 34 ya lashe kambun gwarzon dan kwallon kafar duniya a karo na bakwai.

A yanzu Lionel Messi ya yi wa Cristiano Ronaldo fintinkau wanda shi ma ya lashe kambun har karo biyar.

Sai dai ba wa Messi kambun gwarzon dan kwallon kafar duniya, ya bar baya da kura, inda mutane da dama a fadin duniya ke ganin cewar dan wasan gaban Bayern Munich, Robert Lewandowski ne ya fi dacewa da kambun a bana.

Lewandowski ya yi bajinta wajen zura kwallaye a shekarar 2020, sai dai annobar COVID-19 ta kawo cikas din da ya hana a gudanar da bikin da kuma soke bayar da kyautar a bara.