✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Messi zai bar Barcelona

Lionel Messi zai bar Barcelona bayan shekara 20 yana taka leda a kungiyar

Dan wasan Barcelona, da Ajantina, Lionel Messi ya yi shirin barin kungiyar Barcelona.

Dan wasan mai shakara 33, wanda shi ke rike da kambu Gwarzon Dan Kwallon Duniya, na son barin kungiyar ce bayan kwashe kusan shekara 20.

Rahotanni sun nuna cewa duk da cewa kwantiraginsa zai kare na a kakar badi, Messi na da damar barin kungiyar a bana, kuma a kyauta kamar yadda yarjejeniyar kwantiraginsa ta tanada.

Tun bayan shan kashi da Barcelona ta yi a hannun Bayern Munich ake ta rade-radin cewa Messi na son barin kulob din.

Bayan doke su da aka yi, kungiyar ta sallami kocinta, Quique Setien da Manajan Tsare-tsarenta, Eric Abidal, inda tuni ta maye gurbin kocin da Ronald Koeman.

Wata majiya ta shaida wa Goal.com cewa tuni Messi ya fara bayyana wa ’yan uwa da abokansa cewa zai bar Barcelona.