✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Miji da mata

Wani maigidane bayan ya dawo gidansa daga wajen aiki, ya zauna sai matarsa ta zo ta zauna suka fara hira irin ta miji da mata.…

Wani maigidane bayan ya dawo gidansa daga wajen aiki, ya zauna sai matarsa ta zo ta zauna suka fara hira irin ta miji da mata. Ga yadda hirar tasu ta kasance: Mata: “Maigida, sannu da zuwa.” Miji: “Yawwa uwargida, ya yaran?” Mata: “Lafiyarsu kalau.” Miji: “Allah Ya yi miki albarka.” Mata: “Amin, rabin raina.” Miji: “Uwargida kin ji wani labari da na ji yau?” Mata: “A’a sai ka fada.” Miji: “Yanzu nake jin labarin cewa maigari ya ba da sanarwar cewa duk mai mace daya an ba shi nan da kwana uku ya kara aure, idan ba haka ba za a kashe shi.” Mata: “Alhamdu lillah! Ka ga maigida shi ke nan za ka yi mutuwar shahada.” (Tana nufin gara a kashe shi da a ce ya kara aure, domin ba ta son kishiya).
Daga Isah Ramin Hudu, Hadeja 08060353382