✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Miji ya dauki hayar abokinsa a N10,000 don ya kashe matarsa mai juna biyu

Dubun mutanen biyu ta cika ne lokacin da suka kaure da fada a tsakaninsu.

Dubun wani magidanci mai kimanin shekara 35 ta cika, bayan da jami’an ’yan sanda a Jihar Ogun suka cafke shi saboda zargin daukar hayar abokinsa don ya kashe matarsa mai juna biyu.

An kama Eluyera Wasiu ne da abokin nasa, Adeniyi Samuel, wanda ya dauka don ya kashe matar mai shekara 29 a Karamar Hukumar Shagamu ta Jihar Ogun.

’Yan sanda sun ce dubun mutanen ta cika ne lokacin da baturen ’yan sanda na Ogijo ya samu rahoto daga mazauna yankin cewa wadanda ake zargin na can sun kaure da fada a tsakaninsu.

A ranar Lahadi ne dai ’yan sanda suka samu rahoton cewa Eluyera da Adeniyi na tafka fadan da zai iya kai wa ga jin mummunan rauni ko ma kisa, in ba a raba su ba.

Kakakin ’yan sandan Jihar, Abimbola Oyeyemi, ya shaida wa manema labarai ranar Litinin a Abeokuta cewa bayan samun korafin, DPO na yankin, CSP Muhammed Baba, ya aike da dakarunsa zuwa wajen, inda suka cafko mutanen biyu.

A cewar Kakakin, lokacin da ake musu tambayoyi, Adeniyi ya shaida musu cewa Eluyera ya dauki hayarsa a kan N10,000 don ya kashe matarsa mai juna biyu, mai suna Bola Taiwo.

Ya ce sun amince za a bashi N10,000 ladan aikin, kuma tuni ma aka bashi kafin alkalamin N5,000, bisa yarjejeniyar za a cika masa ragowar da zarar ya kammala aikinsa.

Run da farko dai Eluyera ya bukaci amaryar tasa ne ta zubar da cikin da take dauke da shi, amma ta ki.

“Bayan ya bi dukkan hanyoyin da zai bi amma bai yi nasara ba, sai ya yanke shawarar kawar da ita tare da juna biyun,” inji Kakakin ’yan sandan.

Abimbola ya kuma ce mijin ya yi dukkan dabarun yin amfani da guba wajen kasheta, amma hakarsa ta gaza kai wa ga cimma ruwa, dalilin da ya sa ya yanke shawarar dauko hayar abokin nasa.

Ya ce tuni Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar, Lanre Bankole, ya umarci a gudanar da zuzzurfan bincike domin a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.