✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Miji ya kona matarsa har lahira saboda kin komawa gidansa

Ya bulbula mata fetur ya cinna mata wuta.

Wani magidanci mai suna Ponle Adebanjo, ya kona matarsa Lateefat har lahira bayan da ta guje shi saboda rashin jituwar da ya shiga tsakaninsu.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa wannan mummunan al’amari ya faru ne a ranar Asabar da ta gabata a yankin Otun-Akute, Jihar Ogun.

Mai Magana da Yawun ‘Yan Sandan Jihar, DSP Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar al’amarin a Lahadin da ta gabata.

Bayanan ‘yan sanda sun nuna cewa, an damke wanda ake zargi da aikata danyen aikin ne bayan da makwabta suka kwarmata wa ofishin ‘yan sandan na Otun-Akute abin da ya faru.

“An ruwaito mijin matar, Ponle, ya fada wa jama’a da dama a yankin cewa matarsa ba ta da ‘yancin ta zauna ita kadai, sannan ya sha alwashin babu namijin da zai zauna da ita bayan da ta guje shi.

“Shekara uku ma’auratan suna tare inda suke zaune a yankin Otun-Akute, kafin lokacin da Lateefat ta yanke shawarar ta nisance shi saboda muzguna mata da yakan yi,” inji Oyeyemi.

Jami’in ya kara da cewa, “An ce Mista Ponle ya je har inda matar tasa ke da zama inda ya yi barazanar kashe ta idan ta ki komawa gidansa, tun da bai sake ta ba.

“Makwabtansu sun ce, mutumin ya saba dukan matar, wani lokacin ma kamar zai kashe ta da duka. Sau da dama ana kwantar da ita a asibiti saboda dukan da take sha a hannun hannunsa, kafin daga bisani ta yanke shawarar barin gidan inda ta je ta kama hayar gida ta koma zama ita kadai.

“A ranar Asabar da daddare kuma Mista Ponle ya tafi gidan matar, inda ya tarar da ita tana sallah, a nan ya bulbula mata fetur ya cinna mata wuta.

“Sai dai matar ta samu ta rungumo shi don su kone tare kafin daga bisani makwabta suka ankara aka kai musu dauki, daga nan aka kwashe su zuwa asibiti inda a can ran matar ya yi halinsa saboda kunar wuta.”

Jami’in ya ce daga baya an mika wanda ake zargin ga ‘yan sanda wanda shi ma daga bisani rai ya yi halinsa.