✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mikhail Gorbachev: Muhimman Abubuwa Kan Shugaban Tarayyar Soviet Na Karshe

A ranar Talata ce hukumomin Rasha suka sanar da rasuwar Gorbachev a birnin Moscow, yana da shekara 91 a duniya, bayan ya sha fama da…

A ranar Talata ce hukumomin Rasha suka sanar da rasuwar Gorbachev a birnin Moscow, yana da shekara 91 a duniya, bayan ya sha fama da matsananciyar jinya.

Ga wasu muhimman abubuwa da Aminiya ta tsakuro daga da rayuwar shugaban na karshe na Tarayyar Soviet:

 • Jami’ar IBB ta umarci malamanta su fice daga yajin aikin ASUU su koma aji
 • Kwankwaso 2023: Ba za mu bi Shekarau PDP ba —Kawu Sumaila
 • An haife shi ranar 2 ga watawn Maris, 1931, a kauyen Privolnoye da ke Kudancin yankin Stavropol.
 • Ya fara aiki a shekarar 1946 a wani gidan gona da ke kauyensu.
 • Ya tsunduma harkar siyasa a 1952, da Jam’iyar Kwaminisanci ta zallar masu bin akidar gurguzu.
 • Ya auri masoyiyarsa Raisa Titarenko da suka yi jami’a tare — ta rasu a 1999 sanadiyar cutar Kansa, bayan ta haifa masa ’ya mace.
 • Ya jagoranci Tarayyar Soviet a shekarar 1985-1991, a matsayin babban sakataren jam’iyar Communist.
 • A 1990 bayan kirkirar matsayin, ya zamo shugabanta na farko.
 • Ya kirkiri tsarin perestroika, wanda ya zamanantar da hanyoyin farfado da tattalin arzikin tarayyar karkashinsa.
 • A 1987 shi da shugaban Amurka na lokacin, Ronald Reagan, sun rattaba hannu kan yerjejeniyar ta (INF), don ajiye makamansu na nukiliya.
 • Hakan ya kawo karshen fargabar barkewar yaki tsakanin kasashen biyu.
 • A 1988-1989, Dakarun Soviet a karkshin ikonsa sun janye daga Afghanistan, bayan sun sha kashi a yakin da aka shekaru 10 ana fafatawa.
 • A 1990, an ba shi kyautar Nobel zaman lafiya, sakamakon sauye-sauyen da suka kawo karshen cacar baka tsakanin kasashen Gabas da na Yammacin Turai.
 • A 1991 masu bin tsarin Kwaminisanci sun yi yunkurin kifar da gwamnatinsa, lokacin yana hutu a yankin Crimea. Sai dai ba su samu nasara ba.
 • A watan Disambar 1991 ya ajiye aiki, bayan jagororin kasashen Belarus da Rasha da Ukraine sun amince da narkar da tsarin Soviet.
 • A 1996, ya tsaya a matsayin dan takara mai cin gashin kansa a zaben shugaban kasa, amma ya sha kaya a hannun Boris Yeltsin ya zaben.
 • A shekaru 20 din da suka gabata ya shafe mafi yawan lokacinsa a bayan fagen siyasa, inda ba a cika jin duriyarsa ba.