✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mikhail Gorbachev, Shugaban Tarayyar Soviet na karshe, ya rasu

Ana ganin Mikhail Gorbachev ne ya yi jana'izar Tarayyar Soviet.

Shugaban Tarayyar Soviet na karshe, Mikhail Gorbachev, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekara 91 a duniya.

Kafofin yada labarai na Rasha sun bayar da rahoton cewa Mista Gorbachev ya rasu ne ranar Talata a birnin Moscow.

Kamfanonin dillancin labarai na Interfax da TASS da RIA Novosti sun ruwaito Babban Asibitin Moscow yana sanar da cewa, “Mikhail Sergeyevich Gorbachev ya mutu da yammacin nan bayan ya jima yana matsananciyar jinya”.

Gorbachev, wanda ya yi mulki a tsakanin 1985 da 1991, ya taimaka wajen yaukaka dangantaka a tsakanin Amurka da Tarayyar Soviet.

A shekaru 20 din da suka gabata ya shafe mafi yawan lokacinsa a bayan fagen siyasa, inda ba a cika jin duriyarsa ba.

Sai dai ya yi kira ga Amurka da Rasha su kai zuciya nesa lokacin da sabani a tsakaninsu ya kusa kaiwa na lokacin Yakin Cacar Baka bayan da Rashar ta mamaye Crimea a 2014 da kuma a bana lokacin da ta kaddamar da yaki a kan Ukraine.

Dangantaka mai tsami

Kamfanin dillancin labarai na Faransa, AFP, ya ruwaito cewa a wasu lokuta, dangantaka tsakanin marigayin da Shugaba Vladimir Putin takan yi tsami.

Sai dai kuma duk da haka, Shugaban Kasar na Rasha ya bayyana alhininsa da jin mutuwar Mikhail Gorbachev.

“Da safe(Putin) zai aike da sakon ta’aziya ta wayar tangaraho ga iyalai da abokan (Gorbachev)”, inji mai magana da yawun Fadar Kremlin, Dmitry Peskov.

Tuni dai shugabannin kasashe da hukumomin duniya suka fara aikewa da sakon ta’aziyyar rasuwar Mista Gorbachev.