✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Miliyan 250 sun yi batar dabo a asibitin koyarwa

Hukumar Binciken Cin Hanci da wasu Laifukkan Rashawa Mai Cin Gashin Kanta ta kasa (ICPC) ta bankado sama da fadi da aka yi na Naira…

Hukumar Binciken Cin Hanci da wasu Laifukkan Rashawa Mai Cin Gashin Kanta ta kasa (ICPC) ta bankado sama da fadi da aka yi na Naira miliyan 250 zuwa ga aljihun wasu daidaikun mutane.

An gano hakan ne bayan binciken da jami’anta suka yi kan asusun ajiyar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto (UDUTH) bayan samun bayanan sirri.

Almundahanar ta shafi karkatar da kudaden haraji da ake cira daga albashin ma’aikata karkashin tsarin albashi na bai-daya (IPPIS). Maimakon biyan harajin ga hukumomin gwamanti da ya kamata, sai aka rika karkatar da kudaden zuwa aljifan wasu mutane da wani kamfani.

Kakakin ICPC Rasheedat Okoduwa ta ce an tsare wadanda ake zargin tare da jagoransu wanda jami’i ne a Sashen Kudi na asibitin UDUTH. An kuma kwace motocin alfarma da manyan gidajen da suka mallaka, a kokarin kwato kudaden da aka yi sama da fadi da su.

Rasheedat na zargin sakaci daga hukumar gudanarwar asibitin ta yadda aka samu damar amfani da tsarin IPPIS wurin satar kudaden ma’aikata.

Ta ce wadanda ake zargin sun rika amfani da kafar da Ofishin Babban Akanta na Tarayya ke ba wa hukumomi na gyara kurakurai kafin kammala biyan albashi, suna karkatar da kudaden zuwa aljifansu.

Hukumar asibiti ta yi gum

Duk yunkurin da Aminiya ta yi domin jin ta bakin hukumar asibitin abin ya ci tura, domin  ba ta samu wanda ya amince ya yi mata magana kan lamarin ba.

Wakilinmu ya nemi tattaunawa da Jami’in Kudin da ake zargi da almundahanar, amma ya tarar ICPC ba ta riga ta sako shi ba.

Hukumar asibitin ta turo wani ya ci gaba da aiki a bangaren a madadinsa, sai dai bai fara zuwa ba a lokacin, kamar yadda wata majiya ta sanar da Aminiya.