✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Minista ta gargadi jihohi kan barazanar ambaliya

Ma’aikatar Jin-kai da bayar da Agajin ta shawarci jihohi da su kara zage damtse wajen shawo kan matsalar ambaliya sakamakon yawan ruwan saman da ake…

Ma’aikatar Jin-kai da bayar da Agajin ta shawarci jihohi da su kara zage damtse wajen shawo kan matsalar ambaliya sakamakon yawan ruwan saman da ake samu.

Minista Sadiya Umar-Farouk ta kiraye su da su gano wuraren da za a iya amfani da su wajen tsugunar da mutane na wucin gadi idan aka samu iftila’i.

Ta kuma jajanta wa al’ummar jihohin, Kebbi, Bauchi da Jigawa bisa iftila’in ambaliyar da ta yi sanadiyyar raba su da muhallansu da kuma gonaki.

Sadiya ta ce tuni ta umarci jihohi da su tashi tsaye wajen shirya kayan tallafi domin taimaka wa wadanda lamarin ya shafa.

Ta ce, “Ambaliyar da ta faru a wasu jihohi a kwanan nan na nuna akwai bukatar jihohi su kara tashi tsaye wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’arsu daga matsalar kamar yadda aka yi hasashenta.

“Hasashen yanayin daminar bana ya nuna akwai barazanar ambaliya a jihohi da dama.

“Yana nuna cewa kananan hukumomi 102 a jihohi takwas za su fuskanci ambaliya mai tsanani, yayin da guda 275 kuma za su fuskanci matsakaiciya”, inji Sadiya.

A cewar hasashen, akwai yiwuwar samun ruwan sama mai karfin gaske da zai iya kaiwa ga ambaliya a jihohin Borno, Yobe, Gombe, Adamawa, Taraba, Bauchi, Filato, Nasarawa, Binuwai, Neja, Kogi, Enugu, Anambra, Imo, Abia, Ribas da kuma Akwa Ibom.

Sauran jihohin sun ne Delta, Edo, Ekiti, Osun, Kwara, Zamfara, Sakkwato, Legas, Ondo, Bayelsa, Kaduna, Oyo, Ogun, Abia, Kano, Kebbi da kuma Birnin Tarayya Abuja.