✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Minista ya ba kamfanonin bogi kwangila

Ya ba da kwangilolin tun kafin a tsara su, yana kuma yaudarar mutane cewa ana yin binciken kudi, inji Joy Nunieh, tsohuwar shugabar NDDC.

Tsohuwar Shugabar Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC) Joy Nunieh ta zargi Minista Godswill Akpabio da bayar da gwangiloli ga kamfanoni marasa rajista da karya doka da suka durkusar da ayyukan ma’aikatar.

Joy Nunieh ta ce Akpbio ya sa NDDC ta wa kamfanoni marasa rajista ayyukan tun kafin a tsara su, lamarin ya kawo yawaitar ayyukan da aka yi watsi da su a Neja Delta.

Game da binciken da Shugaba Buhari ya umarci a yi kan kashe Naira biliyan 81.5 cikin wata biyar a NDDC, Joy Nunieh ta ce Akpabio “Yana yaudarar ’yan Najeriya cewa ana binciken kudi. Idan har aka tabbatar da ana gudanar da binciken kudi to a yi watsi da duk abun da na fada”.

Nunieh mai takun saka da Akpabio wanda take zargi da yi mata makarkashiya ta bayyana hakan ne ga Kwamitin Majalisar Wakilai da ke bincikar badakalar kudade a NDDC kai tsaye ta bidiyo.

Dalilin binciken NDDC

Binciken ya bankado ayyuka 150 da hukumar ta yi watsi da su bayan ta biya yawancin ’yan kwangilar karin Naira biliyan biyar-biyar a kan kudin ayyukan.

Da farko binciken kwamitin ya gano yadda NDDC ta yi watanda da sama da Nira biliyan uku da sunan rabon tallafin cutar coronavirus a yankin.

Binciken ya taso ne bayan kwamitin ya gano yadda NDDC ta kashe biliyoyin Naira da suka saba ka’ida da tunani a shekaru, kamar yadda rahotannin Babban Bankin Najeriya (CBN) da Ofishin Babban Mai Binciken Kudi na Tarayya da kuma Hukumar Sayayyar Kayan Gwamnati (BPP) suka bayyana.

A bayaninta, Nunieh ta ce “Babu ko daya daga cikin fitattun kamfanonin binciken kudi da ke Najeriya a cikin jerin kamfanoni tara da za su yi binciken.

“Wasikar Shugaban Kasa ga Majalisar Tarayya ta umarci a yi binciken kudi ta kuma maye gurbin Kwamitin Amintattu da Kwamitin Gudanarwa na Riko da zai lura da binciken

“Amma ministan ya hakikance cewa shi zai lura da binciken, har ta kai ga na tunatar da shi na kuma nuna masa waiksar ta Shugaban Kasa, cewa ba mu da ikon kashe kudade”, inji ta.

Kwamitin ya umarci Akpabio da Mukaddashin Dareka Janar na NDDC Farfesa Kemebradikumo Pondei su hallara a gabansa ta kowane hali zuwa ranar Litinin 20 ga watan Yuli, domin amsa tambayoyi kan kashe kudaden da sauran zarge-zarge da ake wa kwamitin rikon.