✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ministan Birtaniya ya yi Sallah a Masallaci Kudus

Minista Tariq Ahmad ya jaddada goyon bayan Birtaniya kan barin ikon wurare masu alfarma a birnin Kudus a karkasin ikon kasar Jordan.

Ministan Birtaniya kan Yankin Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka da Kudancin Asiya da Majalisar Dinkin Duniya a Ofishin Kula da Kasashe Rainoin Ingilata, Tariq Ahmad, ya yi Sallah a Masallacin Kudus a ziyarar da ya kai ranar Alhamis.

Bayan nuna farin cikinsa bayan ya idar da Sallah a Masallacin da ke Gabashin Birnin Kudus, Minista Tariq Ahmad ya jaddada goyon bayan Birtaniya na barin ikon wurare masu alfarma a birnin Kudus a karkasin ikon kasar Jordan.

“Hakika babbar alfarma ce kasancewa a Masallacin Kudus a wannan safiyar (Alhamis) tare da Daraktan Sashen Wakafi na Birnin Kudus, Sheikh Azzam al-Khatib,” kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.

A halin yanzu, an cimma yarjejeniyar cewa Musulmi za su ci gaba da ibada a Masallacin Kudus, yayin da mabiya sauran addinin ke iya kai ziyara a Masallacin, wanda shi ne na uku wajen matsayi ga Musulumi — Yahudawa kuma na daukar sa a matsayin ainihin wurin bautarsu.

Minista Ahmad ya kuma ziyarci binin Hebron da ke Gabar Yammacin Kogin Jordan, bayan a ranar Laraba ya gana da Ministan Harkokin Wajen Isra’ila, Eli Cohen a Yammacin Birnin Kudus.

Daga nan ya je birnin Ramallah da ke Yammacin Kogin Jordan, suka gana da Ministan Harkokin Wajen gwamnatin Falasdinu, Riyad al-Maliki.

A shekarar 1967 ne Isra’ila ta mamaye Gabashin Kusu a lokacin yakinta da kasashen Laraba, kafin a 1980 ta mayar da yankin karkashin ikonta, matakin da kasashen duniya ba su amince da shi ba.