✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ministan da ya kamu da coronavirus ya koma aiki

Ministan harkonin waje Geoffrey Onyeama ya koma bakin aiki bayan fama da cutar coronavirus. Bidiyon da ke yawo a kafafen zumunta sun nuna ma’aikata na…

Ministan harkonin waje Geoffrey Onyeama ya koma bakin aiki bayan fama da cutar coronavirus.

Bidiyon da ke yawo a kafafen zumunta sun nuna ma’aikata na sowa suna masa barka a lokacin da ya iso ma’aikatar kafin ya wuce ofishinsa.

Wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ya ce “Cikin ikon Allah gwajin #COVID19 da aka yi mini bayan mako uku a killace ya nuna ba na dauke da kwayar cutar”.

A ranar 19 ga watan Yunli ministan ya sanar ta shafinsa Twitter cewa ya kamu da cutar kuma tun lokacin ya kasance a killace kafin warkewarsa.