✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ministan Isra’ila ya kai ziyara masallacin Kudus

Ma’aikatar Harkokin Wajen Falasdinu ta yi Allah wadai da ziyarar.

Ministan Tsaron Kasa na Isra’ila, Itamar Ben Gvir ya kai ziyara a masallacin Al-Aqsa, wuri mai tsarki da ke tsakiyar tashin hankali a gabashin Kudus.

Ministan ya kai ziyarar ce duk da barazanar da Hamas da Falasdinu suka yi tun can da farko kafin ziyarar.

Ziyarar ministan mai tsatsaurar ra’ayi ta janyo martanin mai zafi na bangarorin gwamnatin Falasdinu da Hamas.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Falasdinu ta fitar da wata sanarwar yin Allah wadai da ziyarar a masallacin na Al-Aqsa, abin da ta kira da cewar tsokana ce.

Masallacin da ke a birnin Kudus na cikin yankin Falasdinu wanda Isra’ila ta mamaye tun a shekarar ta 1967.