✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Takardun da ake neman bayani kan N2.2bn sun bace —Minisan Shari’a

Ma'aikatar ta ce ta nemi takardun ko kasa ko sama ta rasa su

Ma’aikatar Shari’a ta shaida wa Majalisar Dattijai cewa kwafin takardun da ta bukata kan amincewar da aka bayar ta fitar da Naira biliyan 2.2 daga asusun SWV, sun bace.

Babbar Sakatariyar ma’aikatar, Beatrice Jeddy-Agba, ce ta sanar da batan takardun, lokacin da ta bayyana a gaban Kwamitin Bin Diddigin Ayyukan Gwamnati na majalisar a ranar Talata.

Kwamitin dai na bincike ne kan zargin da ake yi wa hukumomi da ma’aikatun Gwamnatin Tarayya sama da 200 na salwantar da sama da Naira tiriliyan biyar da suka karba daga SWV tsakanin 2017 zuwa 2021.

A watan da ya gabata ne dai kwamitin ya bukaci Ma’aikatar ta Shari’a da ta bayar da bayanai a rubuce da za su nuna yadda aka amince mata ta fitar da biliyan 2.2 daga asusun.

Beatrice ta shaida wa kwamitin cewa sashen kudi na ma’aiktara sun gaza gano takardun da ake nema.

Sai dai ta tsaya kai da fata cewa ma’aikatar ce ta bukaci fitar da kudin kuma sai da aka bi ka’ida kafin yin hakan.

“Sun duba takardun amma sun kasa gano su. Abin takaici ne. Sashen kula da kudi na ma’aikatar ne ke kula da bangaren. Ina tabbatar muku da cewa an sami amincewa kafin a fitar da kudin, amma ba za mu iya gano takardun ba,” inji ta.

Sai dai Shugaban Kwamitin, Sanata Matthew Urhoghide, ya ce hakan na nufin an kashe kudin ba bisa ka’ida ba.

“Ba mu ga kowacce takardar shaidar amincewa ba. Hakan na nufin an kashe kudin da ba sa cikin kasafin kudi.

“Ba daidai ba ne a ce an kasa gano wadannan takardun. Shawarar da za mu bayar a amatayinmu na kwamiti a karshe ba za ta yi dadi ba,” inji Sanatan.

Kwamitin dai ya ba ma’aikatar karin wa’adin mako daya ta nemo takardun a duk inda suke.