✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ministar Harkokin Mata ta warke daga cutar COVID-19

Ministar ta ja hankalin mutane da su ci gaba da bin matakan kariyar cutar.

Ministar Harkokin Mata a Najeriya, Pauline Tallen, ta warke daga cutar coronavirus bayan shafe kwanaki tana jinya.

Ministar ta bayyana haka ne ranar Litinin a Abuja, inda ta ja hankalin jama’a da su ci gaba kiyaye matakan kariya daga kamuwa da cutar.

Ministar ta yi godiya ga matan Najeriya da daukacin al’ummar kasar da suka taya ta da addu’ar samun waraka bayan an sanar da kamuwarta.

Misis Tallen, ta ce likita ya cewa ba ta dauke da cutar bayan gwajin da aka sake mata, kuma da ita aka yi bikin murnar shiga sabuwar shekarar 2021.

Ta ce za ta ci gaba mayar da hankali wajen kawo abubuwan cigaban mata a kasar nan, da kuma tallafa wa masu rauni da gajiyayyu.

Kazalika, Ministar tana fatan an shiga sabuwar shekarar da kafar dama tare da fatan samun zaman lafiya Najeriya.

A ranar 27 ga Disambar 2020 ne, Misis Tallen ta wallafa a shafinta na Twitter cewa ta harbu da cutar ta coronavirus.