Ministoci 8 da suka halarci zaman Majalisar Zartarwa | Aminiya

Ministoci 8 da suka halarci zaman Majalisar Zartarwa

    Ishaq Isma'il

A ranar Laraba 2 ga watan Satumba, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na jagorantar zaman Majalisar Zartarwa a fadarsa ta Aso Rock Villa da ke birnin Abuja.

An fara gudanar da taro da misalin karfe 10.00 na safiya wanda Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha suke halarta.

Ministoci takwas ne kacal suka halarci taron a babban dakin taro na Council Chambers yayin da ragowarsu da kuma Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Folasade Yemi-Esan ke halartarsa daga nesa ta hanyar bidiyo.

Daga cikin ministocin da suka halarci taron ‘ra’ayal aini’ sun hadar da Rotimi Amaechi na Ma’aikatar Sufuri; Ministan Sufurin Jiragen Sama, Sanata Hadi Siriki; da Ministar Kudi, Kasafi, da Tsare- Tsare, Zainab Ahmed.

Sauran sun hadar da Ministan Shari’a, Abubakar Malami; Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fasola; Ministar Labarai da Al’adu, Lai Mohammed; da kuma Ministan Sadarwa, Dakta Isa Ali Pantami.

Wasu daga cikin ‘yan Majalisar Zartarwar da suka halarci zaman sun hadar da Mai Ba da Shawara kan Harkokin Tsaro na Kasa, Manjo Janar Babagana Monguno da kuma Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.