✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ministocin Buhari da suka fi kwazo —Transparency Watch

Wata kungiyar yaki da cin hanci da rashawa, Transparency Watch, ta bayyana ministocin da suka fi kwazo a Gwamnatin Shugaba Buhari. Kungiyar ta ce Ministan…

Wata kungiyar yaki da cin hanci da rashawa, Transparency Watch, ta bayyana ministocin da suka fi kwazo a Gwamnatin Shugaba Buhari.

Kungiyar ta ce Ministan Matasa da Wasanni, Sunday Dare, da Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi da kuma Ministar Agaji da Kyutata Rayuwar Al’umma, Sadiya Umar Farouk, sun dara sa’o’insu kwazo a wa’adi na biyu na Gwamnatin Buhari.

Kididdigar ta Transparency watchi yi la’akari ne da kwazo a harkokin gudanarwa, rikon gaskiya da amana yayin sauke nauyin da ke kan ministocin wajen inganta rayuwar al’umma daga bara zuwa yanzu.

Akaluman da Shugaban kungiyar, Maxwell Gowon ya gabatar a ranar Lahadi, 23 ga watan Agustan 2020, sun ce Sadiya ta yi zarra wajen gudanar da shirye-shiryen tallafi, musamman na ciyar da dalibai, N-Power.

Ministan Sufuri Amaechi, ya samu lambar yabo a sanadiyar kwazon da ma’aikatarsa wajen shimfida layin dogo da kuma jiragen kasa a sassa daban-daban na fadin tarayya.

A bangaren Ministan Matasa, Sunday Dare, Transparency Watch ta ce ya ciri tuta m—usamman a nasarorin da ma’aikatarsa ta samu wajen kawo shirye-shiryen inganta rayuwar matasa tun daga tushe.