✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Miyagun Kwayoyi: NDLEA ta cafke mutum 130 a Kaduna

NDLEA ta ce ta yi wannan wawan kamun ne a watan Oktoba.

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Najeriya, NDLEA, ta sanar da kama mutum 130 dauke da miyagun kwayoyi a Jihar Kaduna.

NDLEA ta ce ta yi wannan wawan kamun ne a watan Oktoba inda bakwai daga cikin mutanen da ta cafke mata ne.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito hukumar tana cewa kwayoyin da samu a hannun ababen zargin sun kai nauyin kilogram 1,728.536.

Da yake fitar da sanarwar a ranar Laraba, Kwamandan NDLEA reshen Jihar Kaduna, Umar Adoro, ya bayyana cewa sun rushe wurare 20 da suka yi kaurin suna wajen hada-hadar miyagun kwayoyi.

Haka kuma Adoro ya kara da cewa sun yi nasarar rufe gidaje bakwai da ke da alaka da miyagun kwayoyi.

Adoro ya ce hukumar ta kuma gano naira dubu N300 ta takardar naira N1,000 daga wadanda aka kama masu safarar miyagun kwayoyi.

Kwamandan ya ce miyagun kwayoyin da aka kwace sun kunshi ganyen wiwi kilo 1,388.811 sai hodar Iblis ta koken kilo 0.019 da hodar Iblis ta heron kilo 0.001 da Tramadol mai nauyin kilo 7.666.

NDLEA ta ce akwai kuma wasu nau’in kwayoyin da nauyinsu ya kai kilo 331.786 da kuma miyagun magungunan maye da ake harhadawa da nauyinsu ya kai kilo 0.253.

Hukumar ta NDLEA ta kuma ce ta gudanar da tarukan wayar da kan jama’a a makarantun sakandire a Kafanchan da Kaduna da Zariya bayan wasu biranen da garuruwa domin fadakar da jama’a kan illolin miyagun kwayoyi.