✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Miyetti Allah ta gargadi mambobinta kan ayyukan ta’addanci

Muna kira gare su da su guji ayyukan satar mutane, fashi da makami da duk wani nau'in laifuka.

Kungiyar Miyetti Allah ta Kasa (MACBAN) ta gargadi makiyaya da sauran mambobin kungiyar da su guji aikata ta’addanci, satar mutane, da duk wasu nau’ukan laifuka a kasar nan.

Babban sakataren kungiyar, Usman Baba Ngelzarma, ya yi wannan gargadin a ranar Lahadi yayin amsa tambayoyin wakilinmu a Jos, yayin bikin kaddamar da sabbin mambobin kungiyar a jihar Filato, wanda aka gudanar a ranar Lahadi.

Kungiyar ta fada wa mambobin cewa, “MACBAN Kungiya ce wacce ke zaman lafiya kuma bata yarda da aikata laifi ba kuma a shirye take wajen tona asirin bara gurbin cikinta.”

“Muna amfani da wannan dama domin fadakar da dukkan mambobinmu game da abubuwan da ke faruwa a kasar nan a halin yanzu. Muna wayar musu da kai game da lalata gonaki.

“Muna kira gare su da su guji ayyukan satar mutane, fashi da makami da duk wani nau’in laifuka,” in ji Ngelzarma.

Ngelzarma ya jaddada cewa ba kawai sun zo jihar ba ne don kaddamar da shugabannin zartarwa na kungiyar ba, sai dai suna umartarsu da su rungumi zaman lafiya.

Har wa yau, ya bayyana cewa laifukan da ake aikatawa a kasar nan, ba Fulani Makiyaya ne kadai ke aikata su ba kamar yadda wasu ke zargi.

Ya kara da cewa Makiyayi na iya aikata laifi, amma hakan ba yana nufin kowane Bafulatani ne dan kungiyar ta MACBAN ba.

Sannan ya karyata rade-radin da ake na cewa shugabancin kungiyar ya ba wa jami’an tsaro cin hanci domin sakin wasu masu laifi daga cikin ‘ya’yan kungiyar.

.