✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mohammed Salah ya kamu da coronavirus

Salah ba zai buga wasanni hudu masu matukar muhimmanci ga kasarsa da kuma kungiyar Liverpool ba.

Dan wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta Liverpool da kuma kasar Masar Mohammed Salah ya harbu da cutar coronavirus.

Kamuwarsa da cutar za ta hana shi buga muhimman wasanni hudu; biyu wa kasarsa, biyu ga Liverpool a mako biyu da zai kasance a killace.

A ranar Juma’a Hukumar Kwallon Kafa ta kasar Masar, ta ce Salah ya kamu da cutar ne a lokacin da yake buga mata wasa.

Sanarwar da hukumar ta fitar ta ce gwajin da aka yi bayan Salah ya nuna alamun cutar coronaviru ya nuna sauran ‘yan kungiyar ba su da ita.

Kamuwar Mohammed Salah na zuwa ne jajibirin wasan da Masar za ta karbi bakuncin Togo na neman gurbi a Gasar cin Kofin Afirka, wanda za su mayar biki ranar Talata.

A can Ingila kuma ba zai samu buka wasan Liverpool da Leicester a gasar Firimiya ta ranar 21 ga watan Nuwamba ba da kuma wasan Zakarun Turai da za su buga da Atalanta ranar 25 ga watan.

Salah ya zura kwallo takwas a wasanni takwa da ya buga wa Liverpool a kakar bana.