✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Monguno ya bayyana sunayen kungiyoyin da ke daukar nauyin ta’addanci a Najeriya

Fadar Shugaban Kasa ta zayyano sunayen kungiyoyi masu daukar nauyin ta'addanci a Najeriya.

Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkar Tsaro, Manjo-Janar Babagana Monguno (mai ritaya), ya bayyana sunayen kungiyoyin addinin da ke daukar nauyin ta’addanci a Najeriya da kasashen yankin Sahel.

Monguno ya ce daukar bidiyon farfaganda da kungiyoyin ’yan ta’adda suke yi domin nuna kansu a matsayin masu fada a ji a yankin wani yunkuri ne na samun karbuwa a wajen masu goyon bayansu.

Hadimin shugaban kasar ya bayyana cewar kungiyoyin Jama’at Nasr al-Islam Wal Muslimin (JNIM) da Islamic Muslim Support Group (IMSG) da kuma Islamic State in Greater Sahara (ISGS) ne ke daukar nauyin ta’addancin da ake a Najeriya da ma wasu kasashe.

A cewarsa “Ayyukan ta’addanci na ci gaba da karuwa ne sakamakon daukar nauyi da kungiyar ISGS ke yi a kasar Mali da Jamhuriyar Nijar da kuma Burkina Faso.

“Ayyukan kungiyoyi irin su Jama’at Nasr al-Islam Wal Muslimin (JNIM), Islamic and Muslim Support Group (GSIM), ISGS na ci gaba da yin barazana ga zaman lafiyar yankin.

“A Najeriya kuma Boko Haram da kungiyar ISWAP ne suka mamaye ayyukan ta’addanci, musamman a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan.

“Halin da ake ciki a yankin Sahel bai taba yin muni kamar yanzu ba, tashe-tashen hankula na ci gaba da yaduwa, adadin mutanen da ke gudun hijira na karuwa kuma karancin abinci ya ta’azzara fiye da kowane lokaci,” a cewar Monguno.

Sai dai ya ja hankalin malaman addini da su koyar da kyawawan dabi’u da addini ke koyarwa wajen kawo karshen matsalar ta’addanci da ta mamaye wasu yankuna na Yammacin Afirka.

Ya ce akwai yiwuwar ISWAP ta yi kokarin kafa daula don yakar kasashen da ke tafkin Chadi.