✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mota ta kashe dan acaba da fasinjansa a hanyar Legas

Wata mota kirar Honda da ke gudun wuce sa’a ta murkushe wani dan acaba da fasinjansa a babban titin Legas zuwa Ibadan. Kakakin Hukumar Kiyaye…

Wata mota kirar Honda da ke gudun wuce sa’a ta murkushe wani dan acaba da fasinjansa a babban titin Legas zuwa Ibadan.

Kakakin Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) reshen jihar Ogun, Florence Okpe, ya ce hatsarin ya auku ne da misalin karfe 10:55 na safiyar Lahadi, kuma dan acaban da fasinjan duk sun mutu.

Okpe ya ce hatsarin ya ritsa da mutane uku ne, inda biyu daga ciki suka mutu, dayan kuma ya tsira babu rauni ko daya.

“Tukin ganganci ne ya sa motar kin tsayawa har sai da ta yi wannan barnar, kuma a yanzu dai mun mika gawarwakin mutane biyu zuwa dakin adana gawarwaki na asibitin Idera da ke Sagamu,” inji shi.

Okpe ya ce Kwamandan Hukumar Ahmed Umar ya gargadi masu motoci kan gudun wuce sa’a a tituna, tare da mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan.