✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Mota ta kashe mara lafiya a asibitin Jos

Ya je ganin likita ne lokacin da ya gamu da iftila’in

Wani magidanci mai suna Malam Zubairu ya rasa ransa sakamakon bi ta kansa da mota tayi a harabar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH).

Marigayin, wanda mazaunin unguwar Lamingo ne da ke Karamar Hukumar Jos ta Gabas, ya ziyarci asibitin ne saboda rashin lafiyar da yake fama da ita, inda ya ga mu da ajalinsa.

Wani dan uwansa mai suna Abok ya bayyana wa Aminiya cewa marigayin na kan hanyarsa ce ta fita daga asibitin bayan ganin likita, inda ya fadi, motar kuma ta bi ta kansa har ya samu rauni.

Abok ya ce, “Ni na saba kai shi asibiti, amma yau sai bai kira ni na kai shi ba, sai dansa ne a kai shi a babur.

“To ya riga ya ga likitan ma ya fito wurin ajiye ababen hawa don ya dauko babur din su taho gida ke nan ya yanke jiki ya fadi motar kuma ta bi ta kansa har ya samu raunuka.

“Daga nan aka garzaya da shi sashin bayar da gajin gaggawa na asibitin, kuma a can ya ce ga garinku nan.”

Wani ma’aikacin asibitin ya bayyana kaduwarsa da rasuwar magidancin, inda ya ce kowa ya san shi saboda tsarabar da yake yi wa ma’aikatan asibitin duk lokacin da ya je ganin likita.