✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Motar bas makare da ’yan sanda ta fada kogi a indiya

Wata motar bas ta yi ajalin wasu a kalla ‘yan sanda shida tare da jikkata wasu 33 bayan da ta fada cikin wani kogi a…

Wata motar bas ta yi ajalin wasu a kalla ‘yan sanda shida tare da jikkata wasu 33 bayan da ta fada cikin wani kogi a kan hanyarta ta dawowa daga aiki a kasar Indiya.

Hadarin ya afku ne a ranar Talata a yankin Phalagam da ke yakin Kashmir na bangaren Indiya, a cewar kamfanin dillancin labarai na Xinhua na China.

Motar Safar na dauke ne da jami’an tsaron ne da ke dawowa daga aikin samar da tsaro ga masu bautar addinin Hindu wadanda ke wani bikinsu na Amarnath Yatra.

Hatsarin ya faru ne yayin da birkin da motar suke cike ya tsinke, inda a sakamakon haka motarsu ta fada cikin wani ramin kogin da ruwansa ya janye.

Baya ga wadanda suka mutu, wasu karin mutam 33 sun samu raunuka, an kuma dauke su a jirgi mai saukar ungulu zuwa wani asibitin wurin shakatawa na Srinagar da ke bangaren Indiya a yankin Kashmir.