Motocin alfarma ga ’yan Majalisar Kasa | Aminiya

Motocin alfarma ga ’yan Majalisar Kasa

    BALARABE LADAN

A farkon makon nan ne wasu kungiyoyin kare hakkin dan Adam da ke kasar nan suka kai shugabannin Majalisar Wakila kotu da nufin dakatar da su daga yunkurin da suke yi na saya wa ’yan majalisar motoci na alfarma da kudinsu ya haura Naira biliyan biyar.

Sun kai shugabannin majalisar kara a Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ce suna bukatar  lallai kotun ta taka wa ’yan majalisar birki kada su kashe wannan makudan kudin wajen sayen motocin alfarma a daidai wannan lokacin da ’yan Najeriya suke fama da matsanancin talauci.

Majalisar Wakilai dai ta yanke shawarar sayen motoci 400 na alfarma ga ’ya’yanta ne a wani zama na sirri da ta yi a ranar 5 ga Fabrairun nan.

An ce a wannan zama ’yan majalisar sun bukaci a saya musu mota kirar Toyota Camry sabuwar yayi ta shekarar 2020 ce, wadda a halin yanzu ba a fara shigo da irinta kasar nan ba. Kuma kamar yadda wani fitaccen dillalin motocin Toyota a Najeriya ya bayyana, ana sayar da motar Toyota kirar shekarar 2019 a tsakanin Naira miliyan 26.75 zuwa Naira miliyan 36.75 ne, ya danganta da irin tsarinta. Amma kirar shekarar 2020 za ta fi tsada kwarai.

Rahotonni sun nuna cewa ’yan majalisar sun ki amincewa da wata shawara da aka gabatar musu ta sayen motar da Kamfanin Innoson da ke Nnewi a Jihar Anambra ke kerawa, inda suka bukaci a sayo musu wadda aka kera a kasar waje.

A Majalisar Dattawa ma ’yan majalisar sun amince a sayo musu motocin alfarma da aka ce kowace daya kudinta zai kai Naira miliyan 50, wadanda suka ce za su rika amfani da motocin ne wajen gudanar ayyukansu na kwamitocin majalisar.

A Majalisar Dattawa ta 8 da Bukola Saraki ya jagoranta ma an saya wa ’yan majalisar motoci inda aka kashe kudin da bai kasa Naira biliyan 4 ba wajen saya wa kowane sanata sabuwar mota a kan Naira miliyan 36.

A yayin da ’yan majalisar suka gama aikinsu za su tafi sai Hukumar Gudanar da Majalisar Dokoki ta Kasa ta yi musu gwanjon motocin, har ma da kayan ofisoshinsu da nufin sake fitar da wani kudin a sayi wasu sababbi ga sababbin ’yan majalisa da aka zaba.

Wadannan fa su ne wakilan da ’yan Najeriya suka zaba su je su kare muradunsu domin su samu saukin rayuwa, amma sai suka koma suna kare nasu muradun kawai.

Idan har ya zama dole sai an saya musu motocin, me ya sa ba za su amince a saya musu wadanda ake samarwa a Najeriya ba, yadda za su taimaka wajen bunkasa wadannan masana’antu tare da samar da kafofin samun aiki ga dimbin matasan kasar nan ba, amma sai suka bukaci a sayo musu na kasar waje kuma sababbin yayi mafiya tsada?

Idan suna kishin kasa ne ai da kamata ya yi su tabbatar duk kayan gwamnati da aka saya musu an bar wa na baya da za su zo domin su ci gaba da amfani da su, maimakon a yi musu gwanjon komai, sannan a sake kashe kudi wajen sayen wasu.

Abin mamaki shi ne, an haramta wa talakawa cin shinkafa ’yar kasar waje domin ana so a inganta noman shinkafa a cikin gida, amma an an kyale ’yan majalisa su shigo da motoci daga waje, alhali za a iya samunsu a cikin gida.

Irin wannan dabi’a ta son kai ita ake samu a duk bangarorin gwamnati a kasar nan, yanzu an mayar da dukiyar gwamnati ta zama ganima, sai wasoso kawai ake yi, ma’aikata da dama duk wanda ya samu wani gurbi mai maiko sai ya yi ta bushasha, shi ya sanya idan ya bar aiki cikin lokaci kankane sai ka ga ya zama abin tausayi, saboda rayuwar karya da ya dauka ta hanyar cin kamuyamuya a lokacin da yake aiki.

Idan dai da gaske ne ana yaki da cin hanci da rashawa a kasar nan, wajibi a rage barna wajen gudanar da harkar gwamnati, domin sharholiya da almubazzaranci duk nau’o’i ne na rashawa. Kuma ’yan majalisar kasar nan su ya kamata su fara nuna kyakkyawan misali, domin su ne wakilan da mutane suka zaba don su samar da dokokin da za su taimaka wajen inganta rayuwar jama’a da ci gaban kasar nan. Domin haka bai kamata mai dokar barci ya buge da gyangyadi ba.