✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Motocin Buratai sun kashe dattijo a Katsina

A yayin da rundunar sojojin Najeriya suke kokarin ceto rayukan jama’ar da ’yan bindiga suka addaba, sai kuma aka samu rasa ran wani dattijo a…

A yayin da rundunar sojojin Najeriya suke kokarin ceto rayukan jama’ar da ’yan bindiga suka addaba, sai kuma aka samu rasa ran wani dattijo a jihar jihar Katsina.

Dattijon ya rasa ransa ne lokacin da ayarin motocin Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai, suka bige shi a kan babur dinsa a cikin birnin Katsina.

Dattijon mai suna Salisu Ibrahim (Yar Yara) ya rasa ransa ne a hanyarsa ta kai katin gayyatar daurin auren ‘yarsa da za a yi ranar Juma’a mai zuwa.

Wani ganau ya ce ya ga lokacin da ayarin  motocin sojojin da ke gudu suka bige tsohon a kan layin Yahaya Madaki da ke cikin birnin Katsina.

Salisu Ibrahim ya rasa ransa ne sadda ya zo ketare hanya a kusa da Gidan Mani inda motocin suka dake shi kuma nan take ya riga mu gidan gaskiya.

“Motar da ke cikin ayarin da ta bige dattijon dai ba ta tsaya ba ko kuma direban ya nuna nadamar abin da ya faru”, inji shi.

Aminiya ta samu rahoton cewa, Buratai da wasu manyan jami’an tsaron kasar na jihar sama da kwanaki biyu don ziyarar gani da ido da rundunar tsaro ke yi kan yakar ’yan bindiga a jihar.